Motoci 60 sun daki juna saboda hazo a Amurka

Masu kai agaji sun hau kan motoci domin agaza wa wadanda suka makale.

Asalin hoton, YORK-POQUOSON SHERIFF'S OFFICE/AFP

Bayanan hoto,

Masu kai agaji sun hau kan motoci domin agaza wa wadanda suka makale.

Sama da motoci 60 ne suka yi hatsari sakamakon hazo a babbar hanyar jihar Virginia da ke Amurka.

An bayyana cewa ana nan ana gudanar da bincike kan faruwar lamarin.

'Yan sanda sun shaida cewa hazon wanda yake gauraye da yanayin dusar kankara na daga cikin abubuwan da suka jawo hatsarin.

Hatsarin ya afku ne a ranar Lahadi da misalin karfe 8:00.

An shafe sa'o'i da dama kafin a kawar da motocin da suka samu hatsarin da kuma bude hanyar.

Wani direban mota ya shaida wa kamfanin dillancin labarai cewa ya hangi hazo mai yawo a gaba a lokacin da yake tafiya wanda hakan ya sa ya rage gudu, inda ya kunna fitilun motarsa.

Ya ce ''kawai sai na ga motoci sun fara karo da juna suna hawa daya bisa daya.''

Ya ce matarsa ita ma tana kan wannan hanya a wata mota daban kuma hatsarin ya rutsa da ita sai dai ba ta ji rauni sosai ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin motocin da hatsarin ya rutsa da su

Asalin hoton, Reuters