Saudiyya ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa kan mutuwar Khashoggi

An kashe Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kashe Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya tun a shekarar 2018

Wata kotu a Saudiyya ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa sakamakon samun su da laifin kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

Khashoggi, wanda aka kashe a bara, ya shahara wajen caccakar gwamnatin Saudiyya kuma wasu jam'ian gwamnatin Saudiyyar ne suka kashe shi a offishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul na Turkiyya.

Mai shigar da kara na gwamnatin Saudiyya ya bayyana cewa jami'an sun dauki wannan mataki na kashe Khashoggi ba tare da sanin gwamnatin Saudiyya ba, wanda hakan ya ja aka shigar da mutum 11 kara.

Wata kwararriya ta Majalisar Dinkin Duniya ta shaida cewa kisan Khashoggi kisa ne wadda aka yi ba bisa ka'ida ba.

Agnes Callamard a kwanakin baya ta yi kira da a binciki yariman Saudiyya Mohammed bin Salman kan kisan Jamal Khashoggi.

Sai dai Yarima Salman ya musanta zargin da ake yi masa amma a watan Oktoban da ya gataba ya ce ya dauki laifi kan kisan dan jaridar a matsayinsa na babba kuma jagora a Saudiyya.