Rahoto na musamman kan 'annobar' cutar koda a Jigawa da Yobe

Rahoto na musamman kan 'annobar' cutar koda a Jigawa da Yobe

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron rahoton:

Cutar koda ta zamo tamkar wata annoba da ke addabar al’umma a yankunan wasu jihohin arewacin Najeriya, irin su Borno da Yobe da Kano da Jigawa da Adamawa.

Cutar dai tana sanadin mutuwar dubban mutane, da talauta wasu da dama saboda rashin halin daukar dawainiyarta.

Hakan ce ma ta sa wasu daga cikin jihohin suka sa wankin kodar yanzu ya zama kyauta.

Sai dai duk da yadda cutar ke ci gaba da addabar al’umma, har yanzu ba a kai ga gano musabbabin cutar ba.

Yankin Hadeja a jihar Jigawa na cikin wuraren da jama’a suka fi fama da wannan cuta, kuma Muhammad Annur Muhammad ya ziyarci yankin inda ya hada mana rahoto na musamman:

Karin labaran da za ku so ku karanta da suka shafi lafiya