'Kungiyar IS na farfadowa a Iraki'

AFP

Asalin hoton, AFP

Akwai alamu da ke nuna cewa kungiyar nan da ke ikirarin jihadi ta IS na shirin kara farfadowa a Iraki, shekaru biyu bayan kungiyar ta rasa yankinta na karshe da ta yi iko da shi.

Kurdawa da wasu masu leken asiri na kasashen yamma sun shaida wa BBC cewa hare-haren da kungiyar ke kai wa na karuwa.

An shaida cewa mayakan IS din a halin yanzu suna da kwarewa kuma sun fi 'yan kungiyar al-Qaeda illa, kamar yadda wani jami'in yaki da ta'ddanci na Kurdawa wato Lahur Talabany ya tabbatar.

Ya bayyana cewa '' mayakan IS na da dabaru iri-iri akwai kuma kudi a gare su, kuma suna iya sayen motoci da makamai da abinci, suna kuma amfani da makamai na zamani.

''Abin da kamar wuya idan aka ce za a ci galba a kan su.''

Ya ce hare-haren da kungiyar ke kai wa na karuwa a halin yanzu, kuma da alama kungiyar ta kammala sake gina kanta.

Mista Talabany ya ce ''ba kamar magabatansu ba 'yan al-Qaeda, 'yan IS din na boyewa a tsaunukan Hamrin.

''Wannan babbar mabuya ce ga 'yan IS, wuri ne mai sarkakiya da kuma lunguna da yawa wanda zai yi wahala dakarun Iraki su far musu.''

Ya yi gargadin cewa rashin jituwar da ake samu a tsakanin musulmai a Bagadaza za ta zamo wata dama ga kungiyar ta IS din ta kara habaka.

Ya ce ''idan aka ci gaba da samun rashin jituwa, wannan babbar dama ce ga kungiyar IS.''