''Yan Buhari' da masu son a saki Sowore sun yi arangama

Kwamared Deji Adeyanju

Asalin hoton, Twitter

Rikici ya kaure a Abuja tsakanin masu zanga-zangar neman a saki mai jaridar SaharaReporters, Omoyele Sowore da wasu matasa da ake kyautata zaton masu goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari ne.

Rikicin dai ya faru ne a kofar ofishin hukumar kare 'yancin dan adam da ke birnin na Abuja, lokacin da masu son sakin Sowore din suka yi dandazo a ofishin hukumar.

Wani wanda ya shaida faruwar al'amarin ya ce "kwatsam mun taru domin wannan zanga-zanga sai wasu matasa suna wake-waken Buhari suka far mana, inda suka jikkata jagoranmu, Deji Adeyanju."

Ya kara da cewa mutanen da suka 'far musu' sun jikkata Deji inda aka kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.

Kwamared Deji Adeyanju ne yake jagorantar ita wannan zanga-zangar bayan karewar wa'adin mako biyu da ya bai wa gwamnatin Shugaba Buhari da ta saki Omoyele Sowore da sauran masu fafutuka da ke hannunta ba.

An dai ce jami'an tsaro na kallon lokacin da mutanen wadanda aka ce sun kai mutum 60 suka tarwatsa masu zanga-zangar.

A safiyar ranar Litinin din nan Kwamared Deji Adeyanju ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa za su yi zanga-zangar neman bahasi kan wasu mutane da ya yi zargin gwamnati na rike da su.

Omoyele Sowore ya kwashe watanni fiye da uku a hannun jami'an hukumar tsaro ta DSS, bisa tuhumar kokarin yin juyin mulki a Najeriya.

A farkon watan Disambar nan ne Hukumar tsaron ta farin kaya ta sake kama Omoyele Sowore, bayan ta sanar da sakinsa.