Adam Zango ya yi 'kaura' zuwa kudancin Najeriya

Adam Zango ya ce ya bar Kannywood

Asalin hoton, Zango

Fitaccen tauraron fina-finan Hausar nan Adam Zango ya sanar da yin hijra daga arewacin Najeriya zuwa birnin Legas domin 'tsira da lafiyarsa'.

Jarumin wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da jaridar Aminiya ta ranar Juma'a, ya ce ya yanke shawarar barin arewacin Najeriyar ne sakamakon yadda masana'antar fina-finan yankin ta 'ruguje'.

Sai dai Adam Zango ya ce ya bar harkar fina-finan, inda zai mayar da hankali kan wakoki a birnin na Legas.

"Tuni na fara harkokina (a Legas), komai ya kankama. Ina shirin cikin wata shida zuwa shekara ɗaya zan dawo da iyali na gaba ɗaya nan Legas, har da mahaifiyata, cikin yardar Allah."

Dangane kuma da kwarin gwiwar da ya sa jarumin ya koma Legas da sana'a, ya ce " kamar dalibin ilimi ne da ya kammala karatun sakandare idan yana so ya ci gaba da karatu sai ya tafi makarantar gaba da sakandare ko ya je jami'a, wannan ita ce manufata."

Adam Zango ya kara da cewa yana fatan ganin ya yi aiki tare da fitattun mawakan kudancin Najeriya" ina kokarin gana wa da kulla alaka da akalla manyan mawaka biyar a nan Legas."

Da aka tambayi Zango dalilin da ya sa ya bar masana'antar Kannywood, sai jarumin ya ce "dalilin da ya sa na fita, babu abin da ya rage a wannan masana'anta sai zalunci da sharri da cin mutunci a kaina."

A kwanakin baya ne dai fitaccen jarumin fina-finan Hausar, Adam A Zango ya fito karara ya bayyana ficewarsa daga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood.

Bayan fitarsa daga masana'antar, ya bayyana cewa zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Sai dai a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram din a lokacin, Zango ya ce a yanzu ya samar da hanyar da zai rinka fitar da sabbin fina-finansa ta intanet, inda masu kallo za su je su siya kuma su kalla.

A cewar Zango, babu yadda za a yi mutum ya kashe miliyoyin kudi wurin hada fim, kuma ya sake shi kara zube ko ya sa shi a sinima, "da wuya kudaden su dawo".

Da dama daga cikin 'yan kannywood sun dade suna korafi kan satar fasaha ta yadda mutum zai kashe kudi ya yi fim amma daga baya wasu su sace fim din su sayar.