Mota ta fada ruwa ta kashe mutum 26 a Indonesia

Bayanan bidiyo,

Masu aikin ceto na ta kokarin ceto ran wadanda suka rayu

Akalla mutum 26 ne suka mutu sannan 13 suka jikkata bayan da wata motar bas ta yi nutso cikin wani kogi a kasar Indonesia.

A ranar Litinin ne dai motar mai dauke da fasinjoji kimanin 50 ta fada ruwan mai nisan mita 150 a kudancin Sumatra na kasar.

Motar kirar bas dai ta tashi daga birnin Bengkulu inda ta nufi Palembang, tafiyar awoyi masu dama.

Akalla masu aikin ceto 120 ne ke faman laluben fasinjojin da ke cikin ruwan.

Yanzu haka ana ci gaba da binciken abin da ya haddasa hatsarin

Ana dai yawan samun irin wannan hatsari a kasar Indonesia inda mota makil da jama'a ke yin nutso cikin kogi, al'amarin da ke haddasa rayukan jama'a.

Map