Ko sulhu zai yiwu tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi?

  • Usman Minjibir
  • BBC Hausa
Ganduje da Sarki Sanusi

Asalin hoton, TANKO YAKASAI

Kwamitin sulhun da kungiyar dattawan arewa ta kafa domin warware rikici tsakanin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Sanusi, na bai wa masana da masu lura da al'amura kwarin gwiwar karkare wannan zama irin na 'yan marina da bangarorin biyu suka kwashe fiye da watanni biyar suna yi.

Dattawan na arewa dai sun kafa kwamiti ne mai mutum 10 da ya kunshi Alhaji Adamu Fika da Janar Muhammadu Inuwa Wushishi da Farfesa Ibrahim Gambari da Dr Umaru Mutallab da Dakta Dalhatu Sarki Tafida da kuma Sheikh Shariff Ibrahim Saleh.

Sauran 'yan kwamitin wanda tsohon shugaban Najeriya, Abdussalami Abubakar ke jagoranta, su ne gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi wanda shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ne da kuma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

BBC ta tuntubi shugaban wannan kwamiti, Janar Abdussalami Abubakar dangane da abubuwan da kwamitin ya shirya, to amma ya ce kwamitin bai fara zama ba tukunna.

Ya kara da cewa yana kasar Saudiyya kuma yana fatan da zarar ya koma Najeriya, mambobin kwamitin za su shiga aiki gadan-gadan.

Kwarin gwiwa kan Sulhunta Ganduje da Sarki Sanusi

Masana da masu lura da al'amura a birnin Kano da ma Najeriya na dasa ayar tambaya - shin ko wannan kwamiti mai kunshe da gaggan dattawan arewacin Najeriya zai iya sulhunta bangarorin biyu?

Tambayar kenan da ni ma na mika wa wani mai nazari kan gidan sarautar Kano wanda kuma makusanci ne ga fadar.

Masanin wanda ba ya son a kama sunansa ya ce "bisa la'akari da irin manyan mutanen da ke cikin kwamitin, muna da kwarin gwiwar cewa za a cimma matsaya dangane da wannan rikici".

Ya kara da cewa "wani abu ma shi ne dukkannin mutanen guda biyu wato gwamna Ganduje da Sarki Sanusi suna jin maganar 'yan kwamitin."

Sulhun tamkar 'mace ce mai ciki'

Masanin ya ce wannan sulhu zai iya daukar fuska guda uku kamar haka:

  • 'Yan kwamitin za su iya lallashin gwamna Ganduje ya rushe sarakunan guda hudu da ya nada wato na Bichi da Gaya da Rano da Karaye domin komawa kamar yadda ake a da wato Sarki guda daya a Kano.
  • Ko kwamitin dattawan ya ja hankalin Sarki Sanusi ya hakura ya zauna da sarakunan guda hudu da gwamna Ganduje ya nada wato sarakuna biyar kenan a Kano kamar yadda al'amarin yake kafin cire jihar Jigawa daga Kano.
  • Ko kuma idan kwamitin ya so zai iya tsayawa a tsakiya ta hanyar barin Sarki Sanusi a matsayin Sarki mai daraja ta daya, inda su kuma sauran sarakunan guda hudu za su kasance sarakuna masu daraja ta biyu.

'Ba a bari a kwashe duka'

Asalin hoton, Getty Images

Da dama mutane na ganin da wuya a iya tankwara gwamna Ganduje ya soke dukkanin sarakunan guda hudu da ya nada kasancewar bisa al'ada gwamnati ba ta cika amai ta lashe ba.

Hakan ne ya sa wasu ke ganin tasirin da wannan kwamitin na mutum 10 zai yi, bai wuce gargadin Gwamna Ganduje ya mayar da wukarsa cikin kube ta 'yunkurin tsige' Sarki Sanusi ba, sannan kuma a lallashi Sarki Sanusi ya hakura ya tafi da sarakunan guda hudu da gwamnati ta nada.

Masanin tsarin sarautar Kano da ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa " gwamna Ganduje da Sarki Sanusi za su shiga yanayin gaba kura baya sayaki ne kasancewar duk wanda ya bujire wa matakin da kwamitin ya dauka to za a yi masa kallo maras son maslaha."

Wane tasiri sulhun zai yi?

Masanin gidan sarautar Kano ya ce duk matakin sulhun da kwamitin ya dauka daga cikin ukun da ya zayyana a sama to yana da tasiri a kan bangarorin biyu da kuma al'ummar jihar Kano.

Ya ce rikicin dai ya janyo raba zumunci tsakanin 'yan uwa, inda misali aka 'gwara' kan 'ya'yan marigayi Sarki Ado Bayero da na marigayi Sarki Sanusi I.

Har wa yau ya ce " idan ka duba abin da ya faru a Danbatta, an cire Sarkin Bai an sa Wada Waziri wanda dan uwa ne ga Sarkin Bai ka ga kenan zumunci ya rabu."

Sannan duba ka ga yadda aka cire hakimin Minjibir aka dora dagaci ya maye gurbinsa to ka ga ai husuma ta hadu.

Haka kuma idan ka dubi yadda aka hada masarautun da ba sa jituwa wuri daya. Misali ya ya za a yi a ce Wudil na karkashin Gaya? Ko kuma Gwarzo na karkashin Karaye?

Saboda haka wannan sulhu zai yi matukar tasiri a tsakanin jama'a kuma muna matukar farin ciki da shi. Allah ya sa 'yan kwamiti su lalubo bakin zaren."

Wannan ne dai karo na biyu da aka samu rashin jutuwar da ta bayyana karara tsakanin gidan sarauta da fadar gwamnatin Kano, tun bayan irin wadda aka samu a lokacin tsohon gwamnan jihar marigayi Abubakar Rimi da marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

A lokacin ne kan al'ummar jihar ya dare, al'amarin da ya janyo tabarbarewar doka da oda wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar jama'a da dama ciki har da tsohon kwamishina a lokacin, Dr Bala Muhammad.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne sakamakon da wannan kwamiti zai fitar bayan tuntubar bangarorin biyu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Za a iya cewa duk matakin da kwamitin dattawan ya dauka daga cikin guda uku da aka zayyana a sama, zai zama izna ga sauran sarakai da gwamnatocin jihohi masu makwabtaka da Kano.