Buhari ya kara jaddada matsayinsa kan batun tazarce

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Fadar shugaban Najeriya ta sake jaddada cewa Shugaba Buhari ba ya da wata aniya ta zarcewa a matsayin shugaban kasa a karo na uku.

Wata sanarwa ta martani da mai magana da yawun shugaban ya fitar Mallam Garba Shehu ta yi watsi ne da abin da ya kira masu neman jan hankali a kafofin yada labarai kan ikirarin cewa shugaba Buhari na take-taken neman wa'adi na uku.

"Mun sake nanatawa: duk wani ikirari da ke nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai nemi wa'adi na uku karya ne," in ji Garba Shehu.

Fitaccen lauyan nan me fafutukar kare hakkin dan adam a Najeriya, Femi Falana, ne ya fara cewa Buhari na neman wa'adi na uku ta hanyar sauya kundin tsarin mulki da zai ba shi damar tsawaita mulkin nasa.

Sanarwar ta ce Mr Falana na cin gajiyar 'yancin fadin albarkacin baki da gwamnatin shugaba Buhari ta tabatarwa 'yan kasar ne, amma baya ga haka babu wani yanayi ko matsi daga wasu masu ra'ayin yin tazarcen da zai sa shugaba Buhari ya amince da batun.

Kuma game da batun da a ke ci gaba da yadawa, sanarwar ta ce, shugaba Buhari yana kara tunatarwa ga wadanda ko dai suna son wa'adi na uku ko kuma suna yada labarin karya saboda wasu bukatunsu cewa:

"Babu wani yanayi da har zai sa shugaba Buhari ya yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don neman karin wani wa'adi.

"Shugaba Buhari wa'adin mulkinsa na biyu kawai zai kammala da zai kawo karshe a 2023, sannan a yi zabe ba tare zama dan takara ba."

Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Buhari dan dimukradiyya ne, yana kuma mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ba zai sabawa tanadin kundin tsarin mulki ba.

"Kuma Buhari ya kara nanata cewa ba zai nema ba kuma ba zai amince da wa'adi na uku ba."