Tsige Trump: Kan sanatoci a rabe yake

McConnell

Asalin hoton, Getty Images

Ana samun rashin jituwa tsakanin 'yan jam'iyyar Republican mai mulki a Amurka da kuma na jam'iyyar adawa ta Democrats a Majalisar Dattawan kasar sakamakon dokokin da aka gindaya yayin sauraron kudirin tsige Shugaba Trump.

'Yan jam'iyyar Democrats dai na bukatar a bayar da dama domin kawo shaidu da kuma takardu a lokacin da za a saurari karar, inda suka ce wannan ce hanyar da za a yi adalci kawai.

Daya daga cikin jigajigan 'yan jam'iyyar Democrats Chuck Schumer ya bayyana cewa sakon imel din da aka bankado a 'yan kwanakin nan, wanda aka tura wa kasar Ukraine ya sa dole a yi komai a bayyane.

Jagoran jam'iyyar Republican a Majalisar Datawan Amurka Mitch McConnell ya ce bai hana a kira shaidu ba, sai dai yana da shakku kan abin da shaidun za su fada.

A makon da ya gabata ne dai Majalisar Wakilan Amurka ta tsige Shugaba Trump sakamakon samunsa da laifin yin karan tsaye ga dimokuradiyya da kuma saba ka'idojin aiki.

Shugaba Trump ne na uku a jerin shugabannin Amurka da aka taba tsigewa a tarihi.

Sai dai ana ganin da wuya ya sauka daga kujerarsa sakamakon jam'iyyarsa ta Republican ce ke da rinjaye a Majalisar Dattawan kasar kuma a nan ne za a gudanar da muhawarar karshe kan batun tsige shi.

Ana zargin Trump da matsin lamba ga Shugaban Ukraine domin kaddamar da bincike kan abokin takararsa na jam'iyyar Democrats wato Joe Biden.

Ana zargin cewa Mista Trump ya yi hakan ne ta hanyar dakatar da taimakon soji ga kasar da kuma sharadin sai sun bayar da hadin kai zai ziyarci kasar.

Ana sa ran fara muhawarar a watan Janairun 2020, bayan hutun Kirsimati da sabuwar shekara.