'Gwamnati ba ta yi aikin kashi 20 ba na kasafin kudin 2019'

@NigeriaPresidency

Asalin hoton, @NigeriaPresidency

Masana tattalin arziki a Najeriya na nuna shakku kan aiwatar da kasafin kudin kasar na 2020, inda suke ganin kasafin kudin ka iya fuskantar matsala.

Farfesa Nazifi Darma, masanin tattalin arziki kuma malami a jami'ar Abuja ya shaida wa BBC cewa "har yanzu ba a cimma kashi 20 cikin dari na ayyukan da aka ware kudadensu ba a kasafin kudin 2019."

Ya ce dukkan harkokin kasuwanci na cikin gida na da alaka ne da yadda gwamnati ke kasafin kudinta da kuma yadda take kashe kudin.

A ganin farfesan, jinkiri wajen aiwatar da kasafin kudin, yakan zama tarnaki ga masu kanana da matsakaitan sana'o'i, har ma da manya-manyan.

Ya ce "idan aka yi la'akari da yadda wasu kasashe masu tasowa irin su Brazil da Indonesia ke kasafin kudinsu, wanda ya ninninka na Najeriya kuma al'ummarsu ba su kai na Najeriya yawa ba, a iya cewa kasafin kudin ya gaza.

''Amma idan kuma aka yi duba da abin da al'ummomin kasashe ke bayarwa a matsayin haraji, sai ka ce nan kuma 'yan kasa sun gaza, domin tasiri da kuma abin da gwamnati ke kashewa ya ta'allaka ne ga abin da take samu daga ciki da kuma wajen kasarta.''

Ya ce a cikin gida haraji ne babbar hanyar samun kudin shigar gwamnati, to idan ka kwatanta da ma'auni da ake da shi na duniya za ka ga Najeriya na cikin kasashe da ke da karancin biyan haraji da bai kai kashi 10 cikin 100 ba, na karfin tattalin arzikin kasar.

''To dole idan ka kwatanta da wasu kasashe da kuma abin da suke samu, sai ka ga ba kai wa gwamnatin adalci ba in kace ta gaza kai tsaye.''

Da aka tambaye shi hanyoyin tattara harajin sai ya ce "Dole a matsa kan gano inda kudaden harajin da ake karba ke zirarewa, a kuma fara karbar wadanda ba a karba ba a baya.

''A tabbatar mutane za su ga ni a kasa cewa kudaden harajinsu da ake karba ga ayyukan da ake dasu.''

Farfesan ya bayyana cewa ''idan aka yi la'akari da kasafin kudin za a ga akwai tsare-tsaren da gwamnatin ta gabatar kamar "Social Investment Programs" wato ayyukan tallafawa al'umma, kudaden da gwamnatin ta ware suna da yawa, shi ya sa ta kirkiri ma'aikata ta musamman don tabbatar da hakan.