Saudi Arabia: An haramta auren 'yan kasa da shekara 18

Wata mace 'yar Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daga yanzu kotuna na musamman ne za su rika kula da batutuwa irin wadannan a Saudiyya

Ma'aikatar Harkokin Shari'a ta kasar Saudiyya ta haramta aure tsakanin 'yan kasa da shekara 18 sannan ta saka 18 din a matsayin mafi karancin shekarun aure a kasar.

Ministan Shari'a Sheikh Dr. Walid Al-Samaani ne ya bayar da umarnin ga kotuna, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito a ranar Litinin.

Batutuwa irin wadannan za a mika su ne ga kotu ta musamman domin duba su karkashin dokar kare hakkin yara.

Umarnin da ministan ya bayar yana karkashin sakin layi na 16/3 na dokar ta kare hakkin yara wanda ya ce:

"Kafin a kulla yarjejeniyar aure wajibi mutum ya tabbatar cewa auren 'yan kasa da shekara 18 ba zai zama matsala a gare su ba sannan kuma da izininsu aka daura shi, mace ko namiji."

Kasar Saudiyya tana gudanar da sauye-sauye a yunkurinta na sajewa da sauran manyan kasashen duniya da kuma guje wa suka da take sha game da zargin take hakkin dan Adam.