Gwamnatin Najeriya ta amince a saki Dasuki da Sowore

Omoyele Sowore

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin sakin tsohon mai ba da shawara kan tsaro na kasar, Kanal Sambo Dasuki da Omoyele Sowore mai jaridar Sahara reporters.

Ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ne ya bayar da sanarwar a ranar Talata.

Malami ya ce gwamnati ta amince da sakin mutanen biyu ne domin mutunta hukuncin kotuna daban-daban na neman belin da suka yi.

Sanarwar ta ce "ofishina ya zabi ya martaba umarnin kotu, inda kuma a waje daya muna duba yiwuwar daukaka kara ko kuma waiwayar neman beli da kotuna da dama suka yi."

An bukaci mutanen guda biyu da su kame daga aikata abubuwan da za su janyo tayar da zaune tsaye da kuma cikas ga tsaron kasa sannan kuma ka da su yi tarnaki ga shari'ar da ake yi musu bisa dokokin kasa."

Wannan umarnin na gwamnati dai na zuwa ne bayan Kanar Sambo Dasuki ya kwashe shekaru hudu a tsare, inda shi kuma Omoyele Sowore ya kwashe watanni uku a tsare.

Tun a 2015 ne dai Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta kame Sambo Dasuki.

Sau hudu dai kotun tarayyar na bayar da belinsa a baya, haka kuma kotun ECOWAS ma ta bayar da belin nasa sau daya.

Gwamnatin dai ta dade tana cewa tana ci gaba da rike shi ne saboda ta daukaka kara.