DSS ta saki Omoyele Sowore a karo na biyu

Omoyele Sowore

Asalin hoton, Facebook/Omoyele Sowore

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta saki mawallafin jaridar Sahara Reporters ta intanet Omoyele Sowore.

Hakan na zuwa ne bayan da ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami ya umarci DSS su saki Omoyele Sowere da Sambo Dasuki a ranar Talata.

Wannan ne karo na biyu da hukumar ta DSS ta saki Sowore bayan sakin sa na farko da ta yi a ranar 5 ga watan Disambar 2019.

Minista Malami ya bayar da umarnin sakin ne bayan da DSS ta sake kama Sowore a babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar 6 ga Disambar 2019.

Gwamnatin Najeriya ta kama Sowore ne a ranar 2 ga watan Agustan 2019, inda take tuhumarsa da cin amanar kasa, daga baya aka saki shi a watan Disamba, bayan shafe wata uku a tsare.