Burkina Faso: An kashe mata 31 a wani harin masu ta da kayar baya

A soldier of the Burkina Faso army on patrol in Soum province. File photo

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Dakarun tsaro a Burkina Faso sun shafe shekaru suna yaki da masu tayar da kayar baya

Jami'ai a kasar Burkina Faso sun ce wasu da ake zargin mayakan sa kai ne sun kashe fararen hula 35 kuma 31 daga cikin mamatan mata ne, a harin da akai kai wani sansanin soji a kasar.

Sun ce an kuma kashe sojoji bakwai da mayakan sa kan 80 a harin, wanda sojoji suka dakile na ranar Talata wanda aka kai Arbinda, a yankin Soum da ke arewacin kasar.

Shugaba Roch Marc Christian Kaboré ya ayyana kwana biyu na makoki.

Kungiyoyin masu da'awar kafa daular Musulunci sun zafafa kai hare-hare a Burkina Faso da sauran kasashen Yammacin Afirka, a shekaun baya-bayan nan.

Rikicin ya ci gaba duk da kokarin kasashen yamma na taimaka wa gwamnatocin yankin yakar ta'addanci.

A watan Nuwamba sojojin Faransa 13 ne suka mutu a yayin da wasu jiragen helikwafta biyu suka yi taho-mu-gama, lokacin da suke kai wasu hare-hare kan masu tayar da kayar da baya a kudancin Mali kusa da kan iyakar Burkina Faso.

Map

A makon da ya gabata, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi bayani kan yakin da ake da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel, a yayin wata ziyara da ya kai Jamhuriyyar Nijar.

Ya ce: "Hakika makonni masu zuwa za su kasance masu wahala a yakin da muke da ta'addanci."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Gomman mayaka ne a kan babura suka kai harin na ranar Talatar wanda suka shafe sa'o'i suna yi.

Zuwa yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma kuniyoyi masu kawance da al-Qaeda ko IS na da karfi a yankin.

A wata sanarwa da ya fitar, Shugaba Kaboré ya ce: "Wannan mummunan harin ya yi sanadin mutuwar mutum 35, kuma mafi yawan mamatan mata ne."

Ya kuma yabi "gwarazan sojojin kasar" wadanda suka fatattaki mayakan.

A farkon wannan watan ma a kalla mutum 14 aka kashe bayan da 'yan bindiga suka bude wuta a cikin wani coci da ke gabashin kasar.

A baya dai Burkina Faso, wacce kasa ce da Musulmai suka fi yawa na cikin zaman lafiya, amma tun shekarar 2015 ta fara fuskantar tashe-tashen hankula.

Kusan mutum 700 ne suka mutu yayin da aka raba mutum 560,000 da muhallansu.

Rikicin ya yadu ne daga kan iyakar makwabciyar kasar Mali, inda mayaka masu kaifin kishin Islama suka kwace ikon arewacin kasar a shekarar 2012, kafin sojojin Faransa su fatattake su.