Buhari ya jajanta wa Jonathan kan harin 'yan bindiga

Buhari da Jonathan

Asalin hoton, Garba Shehu/Twitter

Bayanan hoto,

Buhari ya jajanta wa Jonathan kan hari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya taya wanda ya gabace shi Goodluck Jonathan jaje kan harin da wasu 'yan bindiga suka kai kusa da gidan Jonathan din a jihar bayelsa cikin daren jiya.

Buhari ya kira Jonathan ta waya inda ya yi masa jaje kan harin da aka kai wa wasu sojoji dake kusa da gidan Jonathan a kauyen Otuoke dake jihar Bayelsa.

Lokacin da aka kai harin dai a daren Talata Jonathan ba ya kauyen, sai dai mai magana da yawunsa ya ce tsohon shugaban ya koma gida da safe domin duba irin barnar da aka yi.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba Buhari ya kuma jajanta wa iyalan sojan da ya rasa ransa a harin.

Buhari ya kuma jaddada samar da karin kariya ga Shugaba Jonathan da ma dukkanin jama'ar kasa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Goodluck Jonathan, Ikechukwu Eze ya fitar, ta ce maharan wadanda suka je garin a cikin kwale-kwale mai inji guda biyar, sun far wa jami'an tsaron ne da misalin karfe 1:30 na daren Talata.

Mutanen sun kai harin ne kan sansanin sojojin mai tazarar mita 100 da gidan Goodluck Jonathan, da manufar kwace jiragen ruwa mallakar sojoji.

To sai dai sanarwar ta ce sojojin sun samu nasarar fatattakar 'yan bindigar bayan fafatawa.

Tuni dai jam'iyyar APC mai mulki ta nemi a gaggauta gudanar da bincike kan harin, domin gano wadanda suka kai shi da kuma wadanda suka saka su.