Gwamnatin Najeriya ta saki Kanar Sambo Dasuki

Kanar Sambo Dasuki ya shafe shekaru hudu a hannun hukumomi
Bayanan hoto,

Kanar Sambo Dasuki ya shafe shekaru hudu a hannun hukumomi

Gwamnatin Najeriya ta saki Kanar Sambo Dasuki mai murabus, tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, bayan shafe sama da shekara hudu a hannun hukumomi.

An sake shi ne bayan sakin dan fafutukar nan mai jaridar nan ta Intanet, Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Kafin sakin nasu gwamnatin ta ja kunnen mutanen biyu da su kame daga aikata abubuwan da za su janyo tayar da zaune tsaye da kuma cikas ga tsaron kasa sannan kuma ka da su yi tarnaki ga shari'ar da ake yi musu bisa dokokin kasa.

A karshen shekara ta 2015 ne gwamnatin Najeriya ta kama Sambo Dasuki bisa zargin karkatar da kudin makamai sama da dala biliyan biyu lokacin gwamnatin PDP, ta Goodluck Jonathan.

Asalin hoton, FACEBOOK/OMOYELE SOWORE

Bayanan hoto,

Gwamnatin Najeriya na zargin Omoyele Sowore da laifin cin amanar kasa

Kotu ta sha bayar da belin Sambo Dasukin, amma gwamnati ta ki sakinsa.

A cewar wani dan uwansa Sanata Umaru Dahiru, an neme su da su cika sharudan belin kafin aka sako dan uwan nasu.

Masu fafutukar kare hakkin bil'adama a Najeriya na zargin gwamnatin Shugaba Buhari da yin biris ga umarnin kotu a dalilin ci gaba da tsare wadanda ta umurta da a saka.

Tun a shekarar 2015 ne hukumar tsaro ta 'yan sandan ciki ko farin kaya wato DSS ta kame Sambo Dasuki.

Kuma sau hudu kotu na bayar da belinsa a baya da ya hada da na kotun ECOWAS. To amma gwamnatin ta ce ta ci gaba da rike Dasuki ne saboda ta daukaka kara.