Yau take Kirsimeti a fadin duniya

Pope Francis

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Fafaroma ya gabatar da jawabin Kirsimetin bana yana cewa Ubangiji yana kaunar kowa ciki har da mafi muninmu

Al'ummar kirista a fadin duniya sun wayi garin yau Laraba cike da farin cikin bikin ranar Kirsimeti don tunawa da zagayowar ranar haihuwar Yesu Kiristi.

Muhimmiyar rana ce da kiristoci ke alfahari da ita, inda a lokacin wannan biki mabiya addinin Kirista kan gudanar da hidimomi na ibada cikin farin ciki da walwala inda ake ado da sabbin tufafi da dafa abinci iri-iri da kuma ziyartar 'yan uwa.

Yayin da ake gudanar da bikin na Kirsimeti a fadin duniya, Fafaroma Francis ya gabatar da jawabinsa, a fadarsa ta Vatican, inda ya fadi wani muhimmin sako da ke cewa Yesu na son kowa da kowa hatta da bara gurbi a cikin al'umma.

Masana na ganin ya fadi hakan la'akari da kalaman da ya furta makon da ya gabata na cewa ba za'a sake kau da ido kan cin zarafi a cocuna ba.

A lokacin da ya ke bayani a gaban dubban mabiya addinin kirista a fadar Vatican,fafaroma Francis ya nemi mabiyan da ka da su ta ba yanke kauna.

Hakama ya bayyana cewa Yesu na son kowa da kowa, na kwarai da bara gurbi cikin al'umma.

Ana ganin jagoran ya yi kalamain ne a matsayin manuniya kan cin zarafin kananan yara da ya yawaita a wasu coci-coci.

Ko a makon da ya gabata ya ce ba za'a sake kau da kai ga cin zarafin yara ba, da sunan boye bayanan su ko kuma kare martabar masu cin zarafin.

A yanzu dai Fafaroma Francis ya sauya wata doka da ke cikin kundin Vatican,da ta sha ta shekarun cin zarafi na farawa daga shekaru 14 zuwa kasa, inda ya maida shekarun cin zarafin sha takwas zuwa kasa.