Abin da ya sa muka saki Sambo Dasuki da Sowore – Malami

Sambo Dasuki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An saki Sambo Dasuki bayan tya shafe fiye da shekara hudu a tsare

Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya ce jin kai da biyayya ga umarnin kotuna su ne dalilan da suka sa gwamnati ta saki tsohon mai ba da shawara ta fuskar tsaro Sambo Dasuki da mawallafin jaridar Sahara Reporters Omowole Sowore.

A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta saki Sambo Dasuki bayan shafe sama da shekara hudu tsare a hannun hukomi bisa zargin cin hanci da rashawa da karkatar da kudin sayen makamai domin yaki da Boko Haram.

A tattaunawarsa da BBC Abubakar Malami ya ce gwamnatin Najeriya ta ga dacewar yin biyayya ga umarnin kotunan kasar da suka bayar da belin Sambo da Sowore, duk da cewa suna da damar ci gaba da tsare su, saboda sun kalubalanci matakin na kotuna.

"Ba ka da wani dalili da za ka ambata a matsayin hujja bayan dalili na sha'awa da da'a da abinda ya danganci doka da umarni na kotu," in ji Abubakar Malami.

Ya kara da cewa an sako su ne "a bisa dalilai na jin kai, duk da yake gwamnatin tarayya tana da hakki na ta ci gaba da rike su a lokacin da take kalubalantar sakinsu, har a kai matika ga kotun koli."

Wasu 'yan Najeriya dai da ra'ayin cewa an saki Sambo Dasuki da Sowore ne saboda matsin lambar Amurka, musamman ganin cewa Sowore yana da shaidar zama dan Amurka.

Tuni dai ake yada wata wasika da aka wasu 'yan majalisar dattijan Amurka ne suka rubuta wa ministan dangane da bukatar sakin Sowore.

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar Yusuf Yakasai da Abubakar Malami kan batun:

Bayanan sauti

Hirar BBC da Minista Malami kan sakin Dasuki

To sai dai Abubakar Malami ya musanta hakan, inda yace babu wani matsin lamba da suka fuskanta daga kowace kasa kafin sakin mutanen.

"Karya ce tsagwaronta cewa ofishin antoni janar ko gwamnatin Najeriya ta karbi wata takarda daga wasu 'yan majalisa ko kuma wasu sanatoci na Amurka."

Ya kara da cewa "Har yau maganar nan da ake babu wata takarda a hukumance da muka karba daga bangaren Amurka ita kanta, dangane da abinda ya danganci wannan mu'amala."

Asalin hoton, FACEBOOK/OMOYELE SOWORE

Bayanan hoto,

Gwamnatin Najeriya na zargin Omoyele Sowore da laifin cin amanar kasa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tun a ranar daya ga Disambar 2015 aka kama Sambo Dasuki bisa zargin amfani da kudin sayen makamai wajen yakin neman zabe.

Kotuna da dama sun bayar da belinsa, amma gwamnati ba ta yi aiki da hukuncin kotunan ba sai yanzu.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam da masu rajin dimokradiyya na yawan sukar gwamnati kan ci gaba da tsare Sambo Dasuki da shugaban kungiyar 'yan shi'a ta IMN shaikh Ibrahim El-zakzaky, da Omowole Sowore, suna cewa gwamnatin ba ta mutunta kutuna sannan tana karen tsaye ga dokokin kasar.

Sai dai Ministan shari'ar Abubakar Malami ya musanta zarge-zargen, inda ya ce gwamnati na mutunta kotuna, kuma gwamnatin na bin hanyoyin da dokokin kasar suka tanada wajen ci gaba da tsare mutanen da ake zargi.

Ya ce gwamnati tana da damammaki da tsarin mulki ya ba ta na yin biyayya ko rashin biyayya ga umarnin kotu.

"Kana da dama ta daukaka kara, kana da dama ta neman kotun da ta yi hukuncin ta sake bin ba'asin hukuncin domin ta yi gyaran fuska a kan hukuncin da ta yi. Har ila yau kana da dama ta dakatar da umarnin da ta yi har ka dauki mataki na gaba."

Ministan ya ce "wannan shi ne abinda gwamnatin tarayya ta yi." Ya kara da cewa magana ta rashin da'a ga umarnin kotu.

Gwamnatin Najeriya ta ce a yanzu za a ci gaba da shari'ar Dasuki da Sowore kan tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Alzakzazy fa?

Sakin Sambo Dasuki da Omowole Sowere ya sa mutane da dama suna tambayar ko yaushe za a saki shugaban mazhabar shi'a ta IMN da gwamnati ta haramta, Shaikh Ibrahim El-zakzaky?

To amma ministan shari'a ya ce gwwamnatin tarayya ba ta da hurumi na yin katsalandan a wata shari'a da take hannun gwamnatin jiha.

"Saboda haka gwamnatin tarayya ba za ta yi katsalandan a kan shari'a wadda hakkin bibiyarta hakki ne na jiha ba."

Gwamnatin tarayya ta sha bayyana cewa ba ita take rike da El-Zakazaky ba, gwamnatin jihar Kaduna ce take tuhumarsa a gaban kotu.

Asalin hoton, Twitter/IMN