Dalilin gwamnatin Najeriya na kin sakin El-Zakzaky tare da su Dasuki

Ibrahim El-zakzaky

Sakin Sambo Dasuki da Omowole Sowere ya sa mutane da dama suna tambayar ko yaushe za a saki shugaban mazhabar shi'a ta IMN da gwamnatin Najeriya ta haramta, wato Shaikh Ibrahim El-zakzaky?

To amma Ministan Shari'a na Najeriyar ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hurumi na yin katsalandan a wata shari'a da take hannun gwamnatin jiha.

A ranar Talata ne gwamnatin ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya DSS umarnin sakin mutanen biyu, amma ban da El-Zakzaky da shi ma ya dade a hannun hukumomin.

Malami ya kara da cewa: "Saboda haka gwamnatin tarayya ba za ta yi katsalandan a kan shari'a wadda hakkin bibiyarta hakki ne na jiha ba."

Gwamnatin tarayya ta sha bayyana cewa ba ita take rike da El-Zakzaky ba, gwamnatin jihar Kaduna ce take tuhumarsa a gaban kotu.

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar Yusuf Yakasai da Abubakar Malami kan batun:

Bayanan sauti

Hirar BBC da Minista Malami kan sakin Dasuki

A baya dai kotu ta bayar da izinin a saki El-Zakzaky da maidakinsa Zinatu, amma hakan ya gagara abinda ya sa ake zargin gwamnatin Najeriya da kin yi wa kotu biyayya.

Ko a ranar 22 ga watan Disamba gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da za ta sanya wa ido bisa zargin take hakkin kowane mutum na yin addinin da ya ga dama, ba tare da wata tsangwama ba.

Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ne ya sanar da sanya Najeriya a jerin kasashen.

Rahoton ya ambato rikicin kungiyar mabiya mazahabar Shi'a Sheikh Ibrahim Elzakzaky ke jagoranta, inda Amurka ta ce rundunar sojin Najeriya da hukumomin tsaron kasar na ci gaba da keta hakkinsu na 'yancin gudanar da harkokin su na addini.

A ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2015, mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya suka hana ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa Janar Tukur Burutai wucewa Zaria, bidiyon yadda sojojin sukai kokarin sasantawa da 'yan Shi'a don su wuce ya karade kafafen sada zumunta.

An yi arangama tsakanin sojoji da 'yan Shi'a, lamarin da ya janyo asarar rayuka. Tun daga lokacin hukumomi ke tsare da Zazzaky da maidakinsa Zinatu.