Burkina Faso: Yadda Musulmai da Kirista 'yan gida daya ke bikin Kirsimeti

Family photo by the gate to the compound

Asalin hoton, Clair MacDougall

Presentational white space

Cikin shekarun nan mabiya addinin Musulunci masu rinjaye sun fuskanci hare-haren masu da'awar jihadi a kasar Burkina Faso.

A daren ranar Kirsimeti mutum 30 ne suka mutu yawanci mata, a harin da mayakan jihadi suka kai kasar.

Sai dai duk da haka akwai wani daddadan labari baya ga na tashin hankali.

Kasar dai tana da dadadden tarihin zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, kuma ba sabon abu ba ne ganin yalan da suka gauraya tsakanin Musulmai da Kirista wadanda suke kashi 23 cikin 100 na al'ummar kasar.

Dan jarida Clair MacDougall ya kai wa irin wadannan iyalai ziyara a birninOuagadougou.

Iris Osnia Ouattara mai shekara biyar ta taso karkashin kulawar iyayenta biyu a Burkina Faso, mahaifinta mabiyin darikar Katolika ne mai suna Desis Ouattara, da mahaifiyarta musulma Afoussatou Sanou.

Lokacin bikin Sallah da ita ake yi, haka ma idan kirsimeti ta zo ana shagalin da ita.

Asalin hoton, Clair MacDougall

A gidansu da ke Ouagadougou, an rataye daya daga cikin hotonta a lokacin tana jaririya tare da fada kirsmeti.

An dauki hoton a shekarar 2015, a wata dabdala da kamfanin siminti da mahaifinta ke aika suka shirya.

Yayin da mahaifinta ke koya mata abubuwan da suka shafi addinin Kirista, mahaifiyarta ma tana koya mata abin da ya shafi addinin Musulunci.

''Tana raka ni masallaci, sannan ta raka mahaifinta coci ranar lahadi,'' in ji Afoussatou.

Asalin hoton, Clair MacDougall

Afoussatou tana salloli biyar a kowacce rana, amma a ranakun Juma'a tana zuwa masallaci tare da Iris.

Haka kuma Iris tana tashi da asubar fari ta yi sallah tare da mahaifiyarta.

''Musulunci addini ne da ke yada zaman lafiya, ba ya takura mutane ko tilasta wa wani abin da bai aminta da shi ba,'' in ji ta.

Asalin hoton, Clair MacDougall

Cikin koyarwar addinin Musulunci a saukake Iris ta koyi yadda ake yin alwala.

Cikin littattafan da suke gidansu, har da na koyarwar addinin Kirista.

Asalin hoton, Clair MacDougall

Denis da Afoussatou na tare da juna sama da shekara shida, haduwarsu ta farko sun yi ta ne a garin toussiana, mai nisan kilomita 55 daga birni na biyu mafi gima a Burkina Faso wato Bobo Dioulasso.

Sun shirya yin aure shekara daya bayan haduwarsu, a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar na addinin Musulunci da Kirista.

Shi ma Denis kamar wasu mutanen ya sauya addini wanda yawancin mabiya Kirista kan yi gabannin aure, musamman idan za su auri Musulma daga bisani sai su koma ruwa.

Asalin hoton, Clair MacDougall

"Mun fuskanci tirjiya daga wasu 'yan uwa a lokacin aurenmu,'' in ji Denis, wanda mahaifinsa ya nuna rashin amincewa.

"An kai ruwa rana daga farko. Mahaifina ba shi da matsala, amma mahaifiyata sam ta ki amincewa,'' in ji Afoussatou.

"Yawancin lokuta idan namiji Kirista ya zo neman auren Musulma, iyayenta ne ba sa amincewa.''

Har yanzu tana kokarin sauyawa mahaifiyarta tunani, don ta amince da aurenta da Denis.

Asalin hoton, Clair MacDougall

Yawancin iyalai a Burkina Faso sun gauraya tsakanin Musulmai da Kirista, kuma suna da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu tare da gayyatar juna wuraren ibada.

Ana yi wa kasar kallon mai dadadden tarihi ta fuskar zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Afoussatou tana da kawaye mabiya addinin Kirista, don haka tun da ba za ta je coci a ranar Kirsimeti ba, za ta zauna a gida don gudanar da shagalin ranar tare da 'yan uwan mijinta.

Ta ce dukkan sha'ani idan ya taso na mabiya addinin Musulunci da Kirista da ita ake yi, daga watan Ramadan, karamar sallah, sallar layya da bikin ista da kirsimeti.

Asalin hoton, Clair MacDougal

A ranar kirsimeti, Majami'ar Immaculate Conception ta mabiya darikar katolika na cika makil da mutane.

Ana sa ran za a girke sojoji a harabar majami'ar da sauran wurare. An sha kai hare-hare a coci da masallatai a baya-bayan nan.

Gabannin wannan rana, limaman coci na gargadin mabiya su kiyaye, kar su yi amfani da manyan jakunkuna, sannan su yi saurin sanar da jami'an tsaro da zarar sun ga wani abu da bai gamsar da su ba.

Asalin hoton, Clair MacDougall

Yawanci mutanen da suke da sha'awar kyale-kyale, kan siyo bishiyar kirsimeti mai fitilu launi-launi a jikinta, da aka kawata ta da dusar kankara ta boge su kuma girketa a wajen coci.

Asalin hoton, Clair MacDougall

A ranar kirismeti, Denis yana daukar Iris zuwa cocin King Christ Parish of Pissy a birnin Ouagadougou, daga bisani baki dayan iyalan gidan ciki har da Afoussatou kan taru a gidan kawun Denis.

''Addini ya koyar damu yadda zamu kaunaci juna, da amici,'' inji Denis. ''Allah ne kadai zai iya mana hisabi.''

Asalin hoton, Clair MacDougall

Iyayen Iris za su ba ta zabin addinin da ta ke son yi idan ta girma, amma a yanzu suna koyar da ita dukkan addinan Musulunci da Kirista.

''Saddini,' in ji Denis yadda ya amince kowa yana da damar yin addinin da ya so.

Asalin hoton, Clair MacDougall

Labari da hotuna daga Clair MacDougall