Taliban 'sun sace' masu macin zaman lafiya a Afghanistan

Masu zanga-zangar People's Peace Movement a Kandahar -a watan Junairu 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Taliban na zargin gwamnatin Afghanistan ce ke daukar nauyin 'yan kungiyar

Taliban ta sace sama da mutum 70 mambobin kungiyar masu fafutuka ta People's Peace Movement, a lokacin da suke kan hanyar zuwa yankin Farah da ke yammacin kasar kamar yadda jami'ai suka sanar.

Kungiyar PPM ta fara maci ne da kiran a dakatar da bude wuta a gundumar Herat makwanni biyu da suka wuce, amma suka yi batan dabo jim kadan bayan shigarsu Farah.

Kawo yanzu kungiyar Taliban ba ta ce uffan kan batansu ba.

Kungiyar Taliban ta fara zaman tattaunawar sulhu da Amurka, amma duk da hakan ta kai hare-hare a cikin kasar da sojojin kasashen waje da ke Afghanistan.

Mataimakin gwamnan Farah Massoud Bakhtawar, ya ce 'yan Taliban sun tsayar da motoci shida da masu fafutukar ke ciki, a manyan hanyoyin kasar, an kuma tasa keyarsu wani wuri da kawo yanzu ba a tantance ba.

A watan Mayun 2019 ne PPM ta fara ayyukanta a yankin Helmand, sun fara da zanga-zangar rashin amincewa da kai hare-hare, bayan wani bam da aka dasa a mota ya tashi a filin wasa tare da hallaka mutum 17 da jikkata farar hula 50.

Tun daga lokacin suka fara gangami a jihohin kasar, ciki har da yankunan da Taliban ke iko da su.

Map

A baya dai Taliban ta sha zargin gwamnatin Afghanistan ce ke daukar nauyin kungiyar PPM, zargin da suka musanta.

Dubban fararen hula da jami'an tsaro da dakarun kasashen waje 3,000 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Taliban ke kaddamarwa a kasar tun shekarar 2001.