Bayanai na kara fitowa kan harin Burkina Faso

Burkina Faso na fuskantar hare-haren ta'addanci sosai daga kungiyoyi
Bayanan hoto,

Burkina Faso na fuskantar hare-haren ta'addanci sosai daga kungiyoyi

Bayanai na kara fitowa kan harin da 'yan bindiga suka kai a Burkina Faso da ya kashe gwamman fararen hula yayin da ake zaman makoki na kwana biyu.

Bayanan da jami'an tsaro suka tabbatar na nuna cewa sama da mahara 200 a kan babura suka kai tagwayen hare-haren dauke da manyan makamai.

To amma kafin sojojin da ke sintiri a yankin su iya tunkararsu tuni sun hallaka jama'a da dama a wani shingen binciken soji da ke yankin Soum.

A Soum din kawai 'yan tada zaune tsayen sun hallaka mutun 35 kusan dukkansu mata, tare da wasu sojoji bakwai.

To sai dai bayan wani kukan-kura ne jami'an tsaron suka samu nasarar kashe 'yan bindigar tamanin, a cewar gwamnati.

A cewar ministan tsaron Burkina Faso Cherif Sy, kasar na neman hadin kan al'umma a yankin matsawar ana son shawo kan ta'addanci a yankin.

Burkina Faso ta zamo kasa a nahiyar Afrika ta baya bayan nan da ke fuskantar haren haren yan bindiga da ke da nasaba da tsatstsauran ra'ayin addini daga wasu kungiyoyi.

Masana na ganin cewa hare-haren ta'addanci na karuwa ne a yammacin Afrika saboda rashin samar da isasshen tsaro daga kasashen.

Ko a 'yan makonnin da suka gabata 'yan bindiga sun hallaka sojojin Nijer 71 a wani hari kan iyakarta da Mali.

A yanzu gwamnati a Ouagadougou ta ayyana zaman makoki na kwana biyu, yayin da ake ci gaba da zaman zullumi a kasar.