Waiwaye kan Gasar Premier bayan kammala zangon farko

Premier Trophy

Asalin hoton, Getty Images

Bayan kammala zagayen farko na wasanni Gasar Premier, abubuwan ban mamaki da ban haushi da ban takaici har ma da ban kunya sun faru a wasanni 190 da aka yi cikin mako 18.

A kan haka ne muka yi waiwaye adon tafiya tare da zakulo muku wasu daga ciki, yayin da ake shirin ci gaba da bai wa hammata iska a tsakanin kungiyoyin 20.

Farkon shekarar 2019 Manchester City ta lashe kofin Gasar Premier shekaru biyu a jere bayan kazamin gumurzu da Liverpool, to amma yayin da City ke mulki a Ingila, Liverpool ta nuna isa a nahiyar Turai.

Wannan ya biyo bayan lashe kofin zakarun Turai da ta yi bayan doke Tottenham 2-0 a birnin Madrid.

Ga wasu daga cikin abubuwan da tarihi ba zai manta da su ba a Gasar Premier ta Ingila ta bana.

Dan wasa mafi bajinta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wilfred Ndidi ya kwato kwallo sau 98, ya kuma mika kwallo ga abokan wasa sau 577, kuma kawo yanzu babu wani dan wasan tsakiya da ya yi nasarar yin wannan bajinta a duniya

Kafin fara wasannin wannan kaka, an yi hasasahen 'yan wasa kamar su Harry Maguire da Manchester United ta siyo fam miliyan 80, da Nicolas Pepe da Arsenal ta biya fam miliyan 72 a kansa da kuma Tanguy Ndombele na Tottenham za su fitar da kungiyoyinsu kunya.

To amma sai ga shi kallo ya koma kan dan wasan tsakiyar Leicester Wilfred Ndidi na Najeriya.

Binciken masana kwallon kafa ya nuna cewa Ndidi da Leicester ta siyo kan fam miliyan 15 kacal daga FC Genk ne ya fi kowane dan wasan tsakiya a illahirin nahiyar Turai kaf, nasarar kwato kwallo tare da mallakar tsakiyar a kan kungiyar hamayya.

Wilfred Ndidi ya kwato kwallo sau 98, ya kuma mika kwallo ga abokan wasa sau 577, kuma kawo yanzu babu wani dan wasan tsakiya da ya yi nasarar yin wannan bajinta a duniya.

A kan haka a ke ta'allaka sirrin nasarar Leicester inda take ta biyu a teburin Premier da bajintar da Wilfred Ndidi ke nunawa.

Jamie Vardy ba ya jin kira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kafin kammala kakar wasannin bara dan wasan gaban Leicester Jamie Vardy ya yunkuro da cin kwallaye

Kafin kammala kakar wasannin bara dan wasan gaban Leicester Jamie Vardy ya yunkuro da cin kwallaye.

Abu kamar wasa, dan wasan na Ingila ya dore da haskakawa kuma kafin kace me, ya zarce sa'o'insa a bana.

Daga farkon shekara kawo yanzu, Vardy na da kwallaye 29, kuma irin yadda Leicester ke cigaba da haskakawa, akwai alamun dan wasan zai kafa sabon tarihin cin kwallaye a Gasar Premier ganin cewa yanzu kakar wasannin ta raba.

A yanzu Jamie Vardy ne ke kan gaba wurin cin kwallaye a kakar wasannin da ake ciki da kwallaye 17, kuma ana ganin zai dora ne inda ya tsaya a wasan da kungiyar ke shirin yi da Liverpool.

Kungiya mafi lalaci - Manchester ko Arsenal?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masana dai sun sallama wa kungiyar kambun kungiya mafi lalaci a bana

Duniya mai yayi! Bayyana kungiyoyin da suka gaza katabus a bana kawo yanzu ba ya bukatar dogon tunani, lura da yadda tsofaffin abokan hamayya da a baya suka hana kowa motsawa a Gasar Premier, wato Manchester United da Arsenal suka kasa komai.

To amma duk da irin lalacewar da kungiyoyin biyu suka yi a wasannin mako 18 da aka buga, masana tamaula na cewa irin yadda Arsenal ta lalace ko a mafarki ba su tsammaci haka ba.

Hakan ya sa kungiyar ta raba gari da mai horar da 'yan wasanta Unai Emery kasa da shekara daya da nada shi, ta kuma maye gurbinsa da Mikel Arteta wanda tsohon dan wasan kungiyar ne.

Ko Arteta zai iya dawowa Arsenal da martabarta? Lokaci ne kawai zai nuna.

Masana dai sun sallama wa kungiyar kambun kungiya mafi lalaci a bana.

Mai horar da 'yan wasan Sheffield ya bayar da mamaki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kara yaba wa Chris Wilder ne ganin cewa yan kudin da kungiyar ta bashi don sayen yan wasa bai taka kara ya karya ba, amma a hakan yake harin zuwa gasar Zakarun Turai

La'akari da cewa a bana ne Chris Wilder ya fara zuwa Gasar Premier a tarihin rayuwarsa, shi ne masana ke wa kallon mai horar da 'yan wasan da ke kan gaba a gasar.

Kafin fara Gasar Premier ta 2019/2020, an yi hasashen cewa Sheffield United na cikin wadanda suka zo rakiya a gasar kuma kafin su kwance kayansu za su koma inda suka fito ne.

To amma babu wanda ya taba tunanin bayan wasannin mako 18 zai ga Sheffield United na biyar a teburin gasar.

An kara yaba wa Chris Wilder ne ganin cewa 'yan kudin da kungiyar ta ba shi don sayen 'yan wasa bai taka kara ya karya ba, amma a hakan yake harin zuwa gasar Zakarun Turai.

Babban abin kunya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shi ne sakamako mafi muni da aka taba samu a cikin shekaru 131 da akayi da fara Gasar Premier

Babban abin kunyar da ya faru a wasanni 190 da aka yi kawo yanzu bai wuce ragargazar da Southampton ta sha ba a hannun Leicester da ci 9-0 har gida.

Shi ne sakamako mafi muni da aka taba samu a cikin shekaru 131 da aka yi da fara Gasar Premier.

Haka ma shi ne wasa na biyu a tarihi da aka taba cin kwallaye biyar kafin hutun rabin lokaci, inda kuma 'yan wasa biyu suka taba cin kwallaye uku-uku a wasa daya (Vardy da Perez).

Zuwan na'urar tantance abinda ya faru lokacin wasa (VAR)

Ci gaba ko ci baya?

Asalin hoton, Getty Images

Idan akwai abinda ya kusa saka hawan jini ga masu horar da 'yan wasa a Gasar Premier ta bana bai wuce na'urar VAR ba.

VAR ba ta zo da kafar dama ba a gasar, la'akari da yadda ta rika kawo rudani a wasanni da dama.

Sai dai a duka kungiyoyin 20 babu wanda na'urar ta so ta ruguza kamar Manchester City da mai horar da 'yan wasanta Pep Guardiola.

VAR ce ta hana kungiyar zuwa wasan kusa da na karshe a gasar Zakaran Turai a lokacin da ta hana ta kwallon da aka tabbatar da saka a ragar Tottenham.

Asalin hoton, Getty Images

Na'urar ba ta tsaya nan ba, ta kuma hana wa kungiyar bugun fenareti har sau biyu a wasanta da Liverpool.

Sau da yawa 'yan wasa sai sun gama murnar cin kwallo, to amma bayan VAR ta sake dubawa sai murna ta koma ciki.

Sai dai bincike ya nuna cewa Tottenham ce ta fi morar wannan na'ura da tuni aka fara kira da a sake sarrafata.

Liverpool lokaci kawai take jira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A yanzu Liverpool na da maki 49 a cikin wasanni 17, kuma ta bai wa mai bin ta wato Leicester City maki 10 a hakan kuma tana da kwantan wasa daya

Maki daya tilo ne tsakanin Liverpool da kofin Premier a bara, wanda daga karshe Manchester City ta lashe.

To sai dai gwuwoyin Liverpool ba su yi sanyi ba, don kuwa har yanzu ba a samu mai iya doke ta ba a bana.

Hasali ma kunnen doki daya kawai ta yi a wasanta da Manchester United.

A yanzu Liverpool na da maki 49 a cikin wasanni 17, kuma ta bai wa mai bin ta wato Leicester City maki 10 a hakan kuma tana da kwantan wasa daya.

Ganin cewa babu wani kofi da kungiyar ta kwallafawa rai kamar Premier a shekaru da dama, da kuma la'akari da yadda tauraruwar kungiyar ke haskawa a bana, masana kwallon kafa na ganin babu tantama wannan shekarar ta Liverpool ce.