Ko Leicester za ta taka wa Liverpool birki?

KOciyan Liverpool Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sau biyu kawai Leicester ta doke Liverpool a shekara 18 a Premier

A tarihi Leicester ta yi rashin nasara a wasa hudu daga cikin biyar da suka hadu a Premier da Liverpool a baya bayan nan, inda suka yi canjaras a daya, inda nasara ta baya baya da suka yi ita ce ta 3-1 a watan Fabrairu na 2017.

Idan Liverpool ta yi nasara a karawar ta Alhamis da Leicester hakan na nufin ta yi galaba a manyan wasanninta uku na waje a jere a karon farko.

Leicester City:

Asalin hoton, Getty Images

Ba a doke Leicester ba a wasannin 11 da ta yi a gida a dukkanin gasa, inda ta ci 8, ta yi canjaras a 3, tun bayan da ta sha kashi 1-0 a hannun Newcastle a watan Afrilu.

A karon farko tun watan Fabrairu an zura wa Leicester kwallo uku a wani wasan Premier, a haduwarta da Manchester City.

Kafin wannan rashin nasara, Leicester ta yi nasara a dukkanin wasanta na Premier tara, inda suka fara ci a kakar nan.

Leicester ba ta yi rashin nasara ba a jere a wasanta na Premier tun was anta uku na karshe a karkashin jagorancin kociya Claude Puel a watan Fabrairu.

Jamie Vardy ya daga raga sau 29 a Premier a 2019 , inda ya zarta wanda ke kusa da shi Sadio Mane, da guda 23.

Vardy ya ci bal biyar a wasansa uku na gida da Liverpool, Andrew Cole ne da Thierry Henry da kowannensu ya ci bal 11, suka zarta shi a bal 7 da ya ci Liverpool a Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fanaretin da James Milner ya ci Leicester ana dab da tashi a wasansu na baya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Liverpool :

A karon farko Liverpool za ta iya yin nasara sau biyar a jere a irin wannan rana ta Boxing Day a wasan Premier.

Reds din sun yi nasara a wasa 29 na Premier a 2019. Sau daya kawai suka zarta hakan a shekara daya, inda suka yi nasara a wasa 33 a 1982.

Liverpool tana saman tebur da tazarar maki 10 a Premier League.

A tarihin babbar gasar Ingila, kungiyar da ta taba samun tazarar maki 10 a lokacin Kirsimeti amma ba ta dauki kofin fa sai Newcastle United a kakar 1995-96.

Liverpool ta yi nasara a wasanta 25 daga cikin 26 na Premier, inda ta yi canjaras a dayan, da suka hada da 16 daga cikin 17 na kakar nan.

Ba a doke Liverpool ba a wasansu na Premier 34, inda suka ci 29, suka yi canjaras a biyar.

Kungiyar ta ci bal biyu ko fiye da haka a wasanta 23 daga cikin 26 na Premier.

Reds din su kadai ne suka yi nasarar jefa kwallo a raga a dukkanin wasanninsu na Premier 17 a bana.

Maki 10 ne tsakanin Liverpool mai 49, ta daya a tebur da Leicester wadda ke mara mata baya da maki 39, yayin da Man City da ke rike da kofi take ta uku da maki 38.

Sauran Wasannin Premier na Alhamis:

Tottenham da Brighton

Aston Villa da Norwich

Bournemouth da Arsenal

Chelsea da Southampton

Crystal Palace da West Ham

Everton da Burnley

Sheff Utd da Watford

Manchester Utd da Newcastle