Abubuwan karfafa gwiwa da suka faru a Afirka a 2019

Dalibai sun daga Peter Tabichi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jajircewa ita ce ta bai wa mutane da dama kwarin gwiwa a wannan shekarar a Afirka.

Mun sake waiwaye kan rayuwar jajirtaccen malamin makaranta, da dalibi da lauya, wadanda suka yi amfani d basira wajen karfafa giwar al'uma a shekarar 2019.

1. 'Matasa suna da amfani sosai'

Brother Peter Tabichi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zabi Peter Tabichi a matsayin gwarzon malamin makaranta na duniya

Ba karamin alfahari ya yi ba a lokacin da dalibansa suka daga shi sama, an yi wa Brother Peter Tabichi gagarumar tarba a kasar Kenya a lokacin da ya dawo daga Hadaddiyar Daular Larabawa, Dubai, inda ya karbo lambar yabo ta zinare a matsayin jajirtaccen malami na duniya.

A watan Mayu ne dai aka ayyana shi a wannan matsayi, bayan alkalai sun tantance, sun kuma yi tankade da rairaya tsakaninsa da sauran malamai kuma shaidar da dalibansa suka yi ce ta kawo shi matsayin.

A hirar da Brother Tabichi ya yi da BBC kan lambar yabon ya ce: "A bayyane take karara matasan Afurka na da bai wa da za su iya sauya duniya.''

Wannan abu ya karfafa wa mutane da yawa gwiwa, ya kuma nuna malami yana taka muhimmiyar rawa wurin sauya rayuwar al'umma ta hanayar ilimantar da su.

Har wa yau, Brother Tabichi yana kokarin karfafa wa dalibansa gwiwa, musamman mata da cusa masu kaunar ilimin kimiyya.

2.Sabuwar uwa, ta kammala makaranta

Almaz Derese

Hakkin mallakar hoto Almaz Derese
Image caption Almaz Derese ta haifi 'yarta Yididiya sa'a daya kafain ta rubuta jarrabawa

Alamu sun nuna babu abin da zai hana Almaz Derese mai shekara 21 'yar kasar Habasha zana jarabawar makarantar sakandare.

A watan Yuni ne, ta fara nakuda sa'a daya gabannin fara jarrabawa.

Ta haifi sankaceciyar 'yarta mai suna Yididiya kuma bayan minti 30 da haihuwar tata ta fara rubuta jarrabawar.

Hakkin mallakar hoto Ilu Abba Bor Zone communication office
Image caption Almaz Derese ta rubuta jarabawa a asibitin Karl Mettu da ke yammacin kasar Habasha

"Saboda zakuwar da na yi na zana jarrabawata, sam ban ji zafin nakuda ba,'' inji Mis Almaz a hirarta da BBC Afaan Oromoo.

Mijinta, Tadese Tulu, ya kai ruwa rana da hukumomin makarantar domin su bar maidakinsa ta rubuta jarabawa a gadon asibiti.

A watan Yuni, ne Mis Almaz ta samu labarin ta samu maki 75 cikin 100 na jarrabawar da ta zana.

Almaz ta ce ba ta taba zaton za ta samu kyakkyawan sakamako kamar haka ba, saboda tana fama da ciwon ciki, ga kuma gajiya da ta yi saboda ba ta jima da haihuwa ba.

"Ba na iya bacci da daddare a lokacin da nake da cikin, sai na ke amfani da lokacin na yi karatu.''

Ta shaida wa BBC nasarar da ta samu na nufin za ta ci gaba da karatu nan da shekara biyu idan ta kammala sakandare, sai ta wuce har matakin jami'a.

Mafarkinta shi ne zama cikakkiyar injiniya.

3. 'Yadda za ka yi zarra'

Jordan Kinyera

Hakkin mallakar hoto Jordan Kinyera
Image caption Shekarar Jordan Kinyera shida a lokacin da aka fara rikicin filaye

Jajircewa, da hazakar karatu a shekarar 2019 ita ce ta shekara ta musamman ga lauya Jordan Kinyera dan kasar Uganda.

A shekarar 1996 Kinyera yana gani aka kwace wa mahaifinsa kadarorinsa a rikicin kwace filaye a shekarar.

Shekara 23 bayan nan babbar kotun kasar ta yanke hukuncin da ya bai wa iyalansa nasara a shari'ar da ka dade ana yi.

''Mahaifina ya yi ritaya, don haka ba shi da kudi sosai,'' inji Mista Kinyera a hirarsa da BBC a watan Afirilu a lokacin da yake magana kan gagwarmayar da ya sha.

Abin takaicin shi ne shari'ar ta dauki lokaci kuma hakan ya sa mahaifin Kinyera bai mori komai ba.

Tsohon mai shekara 82, yana fama da ciwon mantuwa, ''a kodayaushe sai mun tuna masa wani abu da ya faru,'' inji Kinyera.

Matashin lauyan yana yi wa jama'a shela musmman wadanda suke da matsalar fili kamar mahifinsa.

Jajircewr da ya yi, da wallafa labarinsa da sashsen BBC Africa ya yi a shafin sada zumunta na Facebook ya ja hankalin jama'a sosai.

4. 'Jakadan Afirka abin alfahari'

Ndlovu Youth Choir

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ralf Schmitt mai gabatar da shirin America's Got Talent tare da uku daga cikin matasan shirin

"Wannan shekara ta kasance ta musamman cike da nasara," inji mai gabatar da shirin South Africa's Ndlovu Youth Choir, Ralf Schmitt, da ake yi na mawaka.

Abubuwa sun sauya matuka, a lokacin da kungiyar matasan mawakan daga wani kauye da marasa galihu ke rayuwa ta shiga gasar talabijin ta America's Got Talent da ake yi a Amurka.

Mawakan sun yi nasarar kai wa zagaye na karshe a gasar a watan Satumba.

Kafin nan kusan daukacin 'yan Afirka ta Kudu sun mara masu baya.

Mawakan sun rera wata tsohuwar waka ta Afirka wadda ta yi tashe a Amurka a shekarar 1980 mai salon wakar Toto, alkalai da 'yan kallo baki daya sun tsuma.

Kungiyarsu ta wallafa a shafin twitter ''A daren nan muna alfahari da ku jakadun daukacin Afirka.''

5. 'Ni dan aike ne'

Alfred Brownell

Hakkin mallakar hoto Goldman Prize

"Ni dan aike ne, wadanda suka yi nasara su ne al'umma,'' lauya kuma mai fafutika dan kasar Liberiya Alfred Brownell, shi ne ya shaida wa BBC haka a watan Afirilu, bayan ya yi nasarar daukar kyauta ta musamman kan muhalli.

An bai wa Mista Brownell kyautar ne saboda aikin da yake yi tukuru da ya tserar da dajin da ya kai girman eka 500,000 daga lalacewa a kasar Liberiya.

Mista Brownell ya yi aiki kafada da kafada da shugabannin yankin, sun hana kamfanin yin manja na Golden Veroleum Liberia gudanar da aiki a dajin.

Saboda aikin da ya yi, babban kamfanin da ke sa ido na samar da manja mai kyau mai suna Sustainable Palm Oil, ya dakatar da aikin tare da bukatar kamfanin GVL Freezing su dakatar da aikin cire bishiyoyin kwakwar manja, da kuma dakatar da aiki a wajen a nan gaba.

"Lokaci ya yi da ya kamata a hada kai, kama daga kamfanonin manja, da masu zuba jari don su fara yin wasu ayyuka da al'ummomin yankin za su ci gajiyarsu, da ba su kariya da sama masu aikin yi,'' inji Brownell a hirarsa da shirin radiyo na BBC Newsday .

Labarai masu alaka