Dandazon mutane sun kalli kusufin rana mai kama da zoben wuta

Yara sanye da bakin tabarau na musamman dan kallon ''wutar zobe'' ta kusufin rana a garin Wan Twin, Myanmar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yara sun sanya bakin tabarau domin su kalli kusufin rana a garin Wan Twin na kasar Myanmar

Al'umma a yankin Asiya sun kalli yadda kusufin rana na shekara-shekara, wanda aka yi wa lakabi da "ring of fire" da Ingilishi - wato ''zoben wuta''.

Dandazon mutanen sun taru domin kallon abin al'ajbin a kasashe dabn-daban ciki har da Sri Lanka, da Indonesia, da Indiya da kuma Saudiyya.

A kusufin da wata ke yi duk shekara, wata yana mamaye tsakiyar rana, inda yanayin ke kama da zobe.

Akalla ana yin kusufin rana sau biyu a kowacce shekara, suna faruwa ne idan inuwar wata ta lullube duniya.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Yadda rana ta yi kusufi a tsakiyar kasar Myanmar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wata yarinya ta kare idanunta don kallon kusufin rana ta jikin katin hoton kashi na X-ray a birnin Islamabad na kasar Pakistan

Kusufin rana na baya-bayan nan an yi shi ne a ranar 2 ga watan Yuli, ya kuma fito baro-baro ana gani har a kudancin Amurka.

Ana sa ran kusufin rana na gaba za a gan shi a ranar 14 ga watan Disambar 2020, za kuma a gan shi baro-baro a kudancin kasashen Chile da Argentina da kuma kudu masu yammacin Afirka da Antarctica.