'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 14 a Nijar

Sojin Niger
Bayanan hoto,

Maharan sun yi wa jami'an tsaron kwanton bauna a jihar Tillaberi

Masu tayar da kayar baya sun kashe sojoji 14 a lokacin da suka yi masu kwanton bauna a jihar Tillaberi da ke Jamhuriyar Nijar.

A wata sanarwa da ma'aikatar cikin gida ta fitar, ta tabbatar da mutuwar 'yan sanda bakwai da soja bakwai a fafatawar da suka yi da 'yan tayar da kayar baya a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce jami'in tsaro guda ya bata, ya yin da su ma 'yan tayar da kayar bayan suka yi asarar mutanensu, sai dai ba a bayyana adadin wadanda aka kashe ba.

Jami'an tsaron dai suna yi wa tawagar masu yi wa 'yan kasa rijistar zabe rakiya ne a gundumar Sanam gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu da za a yi a shekarar 2020.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen yankin Sahel da ta dade tana fama da hare-haren 'yan bindiga da mayaka masu ikirarin jihadi na ISWAP da 'yan Boko Haram daga makobciyarta Najeriya.

Ko a ranar 10 ga watan Disamba, sojojin kasar 71 aka kashe a jihar Tillaberi, a lokacin da daruruwan mayakan jihadi masu alaka da kungiyar IS da ke yammacin kasar Mali suka kai masu hari a sansanin soji ta hanyar yi masu ruwan bama-bamai.

Wannan shi ne hari mafi muni da aka taba kai wa Nijar, tun bayan yaduwar ayyukan 'yan bindiga a Mali a shekarar 2015.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin rundunar hadin gwiwa ta yaki da mayakan jihadi da ake kira G5, ciki har da kasashen Burkina Faso, da Mali, da Chadi da Murtaniya.