IS ta fitar da bidiyon kisan 'Kiristoci' ne 11 a Najeriya

Wasu mayaka masu ikirarin jihadi

Asalin hoton, AFP/BOKO HARAM

Bayanan hoto,

Kungiyar ta masu ikirarrin jihadi ta samu gindin zama a yankin Afirka ta Yamma bayan tarwatsa ta a yankin tekun Fasha

Kungiyar IS ta fitar da wani faifan bidiyo, wanda a cikinsa take nuna kisan wasu mutane 11 da ta ce Kiristoci ne a yankin arewa maso gabashin Najeriya ne, domin ramuwar gayyar kisan shugabanta da kuma kakakinta a watan Oktoba.

Bisa ga dukkan alamu kungiyar ta IS ta fitar da hoton bidiyon kisan ne a jiya Alhamis 26 ga watan Disamba, washegarin Kirsimeti, domin ya zo daidai da lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Kungiyar ta fitar da bidiyon kisan mai tsawon dakika 56, ta kafarta ta watsa labarai, Amaq kuma aka watsa shi ta manjaharta ta aikawa da sakonni, Hoop da sauran kafofin kungiyar na intanet.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mayakan IS sun tsananta hare-hare a Najeriya da sauran kasashen yankin Sahel

Sai dai babu wani cikakken bayani da kafar da ta fitar da bidiyon ta bayar game da mutanen da aka hallaka din, wadanda dukkaninsu maza ne.

Illa dai ta ce an kama su a cikin makonnin da suka gabata a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda kungiyar Boko Haram, ko IS take da tasiri sosai a kasar.

Hoton kisan wanda aka yi a wani fili ya nuna mutane 11 da aka daure musu fuska, kowannensu sanye da kaya mai launin ruwan goro, durkushe a kasa, sannan kuma ga mayakan kungiyar ta IS 11, sanye da tufafi iri daya masu launin kasa su ma tsaye a bayan kowa ne daya.

Asalin hoton, BOKO HARAM

Bayanan hoto,

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Daya daga cikin mayakan na IS ya karanta wani sako a cikin harshen Hausa. Hoton bidiyon yana kuma dauke da rubutun Larabci na fassarar sakon da mai gabatarwar ke fada.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A maganganun da ke ciki, yana cewa wannan sako ne ga Kiristoci na duniya.

Ya ce: ''Wadannan da kuke gani a nan gabanmu Kiristoci ne, wadanda za mu zubar da jininsu domin ramuwar gayyar rayukan malamai masu daraja, Sarkin Musulmi (wato Abu Bakr al-Baghdadi) da kuma kakakin Daular Musulunci (IS), Abu al-Hasan al-Muhajir."

An dai kashe shugaban kungiyar ta IS ne al-Baghdadi da kakakinta a Syria a kusan karshen watan Oktoba.

Bayan kusan wata biyu kuma a ranar 22 ga watan nan na Disamba, sai kungiyar ta IS ta kaddamar da abin da ta kira ramuwar gayyar kisan mutanen biyu, kuma tun daga sannan ta rika kai hare-hare a kasashe da wannan niyya.

Bayan da wannan mai Magana a bidiyon ya kammala jawabin nasa ne sai aka harbe daya daga cikin kamammun, yayin da wadanda ke bayan sauran goman suka kwantar da su a kasa suka daddatse kawunansu.

Kamar yadda kungiyar ta IS ta yi a wani hoton bidiyo da ta fitar a watan Fabrairu na shekara ta 2015, da ke nuna yadda ta kasha Kiristoci Kibdawa 'yan Masar da ta kama a Libya.

'Yan sa'o'i kafin kungiyar ta IS ta fitar da hoton bidiyon na jiya, dan jaridar nan na Najeriya Ahmad Salkida ya fitar da wani sako a shafinsa na tuwita (Twitter), game da bidiyon.

Kungiyar ta IS a baya bayan nan ta zafafa kai hare-hare a Najeriya da sauran wasu kasashen Afirka ta Yamma.