Hazard zai yi jinya mai tsawo, Xhaka ya tabbatar da barin Arsenal

Hazard bai samu buga wasan hamayya na El-Clasico ba da Barcel;ona saboda rauni da ya samu.
Bayanan hoto,

Hazard bai samu buga wasan hamayya na El-Clasico ba da Barcelona saboda rauni da ya samu.

Eden Hazard na Real Madrid ba zai dawo jinya ba har sai farkon watan Fabrairu kamar yadda jaridar Mail ta ruwaito.

Hazard bai samu buga wasan hamayya na El-Clasico ba da Barcelona saboda rauni da ya samu.

Dan wasan tsakiyar Arsenal Granit Xhaka ya amince da kulla yarjejeniya da Hertha Berlin ta Jamus (Blick).

Mai horar da 'yan wasan Arsenal Mikel Arteta na shirin kawo Adrien Rabiot daga Juventus (Times).

Ita ma Chelsea na sha'awar dauko dan wasan PSG Julian Draxler na Jamus da kuma Idrissa Guaye na Senegal (Star).

A wata mai kama da haka Chelsea na tattaunawa da Willian kan yiwuwar tsawaita zamansa a kungiyar.

Kociya Carlo Ancelotti na Everton ya fara da sa'a bayan da ya yi nasara kan Burnley da ci daya mai ban haushi.

Mai horar da Crystal Palace ya ce zai sayi 'yan wasa hudu zuwa biyar a watan Janairu (Mail).

Eden Hazard na Real Madrid ba zai dawo jinya ba har sai farkon watan Fabrairu (Mail).

Dan wasan tsakiyar Manchester City Leroy Sane na nan daram a kungiyar, duk da ana hasashen Bayern Munich za ta taya dan wasan kan fam miliyan 85 (Star).