Mutum 15 sun mutu a hatsarin jirgin sama a Kazakhstan

Bayanan bidiyo,

Kalli wurin da jirgin mai dauke da fasinjoji kusan 100 ya fadi

Wani jirgin sama ya fado a Kazakhstan, inda akalla mutum 15 suka mutu sannan gommai suka jikkata.

Jirgin dai na Bel Air ya taso ne daga Almaty - birnin da ya fi kowanne girma a Kazakhstan, inda ya tunkari Nur-Sultan, babban birnin kasar to amma sai ya rikito jim kadan bayan tashinsa.

Yanzu haka fasinjoji 60 da suka tsallake rijiya da baya na karbar magani a asibiti..

Har kawo yanzu dai ba a iya tantance hakikanin abin da ya haddasa hatsarin jirgin ba.

Sai dai wani dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Reuters wanda ya kasance kusa da inda hatsarin ya faru, ya ce akwai dusar kankara sosai a wurin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jirgin dai ya fado ne dab da wani gini mai hawa biyu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban Kazakhstan ya ce "duk wanda aka kama da hannu a afkuwar al'amarin za a hukunta shi."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lokacin da fasinjoji ke hawa jirgin kenan a birnin Almatyt