Waiwaye kan abubuwan da suka faru a 2019 a Najeriya

A Najeriya, muhimman al`amura da dama sun faru a kasar a shekarar 2019 mai karewa- ciki har da babban zaben kasar, inda shugaban Muhammadu Buhari na jam`iyyar APC ya sake darewa karagar mulki, da kuma batutuwan da suka shafi shari`a da tsaro da kuma zamantakewa.

BBC ta kutsa cikin kundin ajiyarta inda kuma ta tattaro muku batutuwa kamar haka:

Shugaba Buhari ya sake lashe zabe

Zaben da aka yi a watan Fabrairun da ya wuce za a iya cewa na daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da suka faru a cikin wannan shekara mai karewa a Najeriya.

Hukumar zaben Najeriya ta ce shugaba Buhari na jam`iyyar APC ne ya lashe zaben 2019 bayan ya samu kuri`a fiye da miliyon 15.

Hakan na nufin Buhari ya kayar da babban abokin hamayyarsa na PDP Atiku Abubakar, kasancewar Atiku Abubkar din a cewar hukumar ya samu kuri`a fiye da miliyon 11 ne.

Kodayake jam`iyyar PDP ba ta amince da sakamakon ba, sakamakon zargin da ta yi cewa an tabka magudi.

Wannan ne ya sa ba ta tsaya ko`in aba sai gaban kotun sauraron kararrakin zabe, inda aka yi ta buga shari`a har sai da aka dangane da kotun kolin Najeriya, wadda a karshe ta tabbatar wa shugaba Buhari zabensa.

Zaben jihohi na 'Inconclusive'

Har wa yau, a babban zaben Najeriyar, kallo ya koma jihar Kano sakamakon zubar-gadon da aka yi a zaben gwamna, wanda aka fi sani da 'inconclusive', inda jam`iyyar APC ta kai bantenta, amma da jibin-goshi.

Kazalika a zaben gwamnonin ne jam`iyyar PDP ta kwace jihohin Bauchi da Zamfara da ke arewacin Najeriya. Kodayake daga bisani, a karshen shekara ita ma APC ta yi nasara a jihohin Bayelsa da Kogi, duk kuwa da cewa abokan hamayya suna kalubalantar sakamakon zaben a kotu.

Ganduje ya kirkiri sabbin masarautu hudu

Jim kadan bayan zaben jihar ta Kano sai batun kirkirar sabbin masarautu ta kunno kai inda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi har sau biyu a cikin shekara daya.

Kotu ce dai ta soke kirkirar masarautu hudu da majalisar dokokin jihar ta yi tun da farko, da suka hada da Karaye da Bichi da Gaya da kuma Rano.

Kotun ta ce ta rushe masarautun ne saboda ba a bi hanyar da ta dace ba wajen kafa su, amma daga baya gwamnati ta sake mika wa majalisa bukatar kafa masarautun, kuma ba ta tsaya wata-wata ba ta zartar da dokar sake kafa su, duk kuwa da cewa wasu sun kalubalanci yunkurin a kotu.

Gwamnati ta haramta IMN ta Elzakzaky

Hakkin mallakar hoto OTHERS

A watan Yulin 2019 ne gwamnatin Najeriya ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement In Nigeria da na 'ta'addanci kuma haramtattu'.

Kafin nan dai sai da 'yan sanda suka 'kashe' 'yan kungiyar 11 a Abuja a irin wannan zanga-zanga, inda su kuma 'yan sanda suka yi zargin 'yan kungiyar sun kashe babban jami'n 'yan sanda, a karon farko.

Wani batun shara`a da ya ja hankali a shekarar 2019 shi ne batun belin da wata babbar kotu a Kaduna ta bai wa jagoran `yan kungiyar Islamic Movement da gwamnati ta soke, wato Sheikh Ibrahim Elzazaky da maidakinsa domin su tafi kasar Indiya neman magani bayan kwashe lokaci mai tsawo ana neman wannan damar.

To sai dai a karshe, za a iya cewa wannan damar ba ta yi rana ba, kasancewar haka suka je Indiya suka koma Najeriya ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.

Shari'ar Najeriya da P&ID

A watan Agustan da ya wuce wata kotun Birtaniya ta yanke wani hukuncin da ya kada-hantar gwamnatin Najeriya, kasancewar ta bai wa kamfanin P and ID izinin kama kadarar gwamnatin Najeriya da ta kai dala biliyon tara a ko ina a duniya a matsayin hakkin kamfanin sakamakon rashin cika ka`idar yarjejeniyar wata kwangila tsakanin kamfanin da gwamnatin Najeriyar.

Gwamnatin Najeriya dai ta daukaka kara, cike da fatan cewa za ta samu mafita a wannan shari`ar.

Yawaitar garkuwa da mutane

Duk da cewa an yi fama da wasu hare-hare irin na masu ta-da-kayar-baya a Najeriya, matsalar satar mutane ta fi munana a wannan shekarar, kasancewar an shiga har mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wato birnin Daura aka sace magajin garin, Alhaji Musa Umar wanda ba a samu ceto shi ba sai bayan wasu watanni.

'Yar Najeriyar da ta tsira daga kisa

Hakkin mallakar hoto OTHERS

Kazalika a 2019 ne wata yarinya `yar Najeriya mai suna Zainab ta yi nisan-kwana, bayan da gwamnatin Najeriya ta yi nasarar ceto ta daga hannun mahukunta a kasar Saudiyya, wadanda suka tsare ta bisa zargin shiga kasar tasu da miyagun kwayoyi.

To sai dai bayan an gudanar da bincike aka samu ba ta da laifi.

Jami'an DSS sun kama Sowore

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A watan Agustan da ya wuce ne jami`an hukumar tsaro ta DSS suka cafke mai kamfanin jaridar nan ta Sahara Reporters, Omoyele Sowere bayan wani gangami da ya hada da niyyar kada guguwar juyin-juya-hali.

An dai gurfanar da shi gaban kuliya har kotu ta ba da belinsa, amma rundunar DSS ta ci gaba da tsare shi bisa zargin cewa ya saba wa ka`idar belin.

Masu fafutukar kare hakki a Najeriyar sun yi ta zanga-zanga, tare da samun goyon bayan wasu kasashen duniya.

To sai dai a karshen wannan watan na Disamba gwamnatin Najeriyar ta ba da umurnin a sake shi tare da tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar, Sambo Dasuki.

Najeriya ta rufe iyakokinta

Wani mataki da mahukunta a Najeriya suka dauka na rufe iyakokin kasar ya ta da hankalin al`ummomi mazauna kan iyaka da kuma kasashe makwabta.

Mahukuntan Najeriyar dai na zargin cewa kasashe makwabta ba sa bin ka`idoji ko yarjejeniyar kasuwanci irin na kasashe makwabta, don haka suna jefa Najeriyar cikin hadari ta fuskar tsaro da tattalin arziki.

Sai dai al`ummar kan iyakar na kukan cewa rayuwarsu na tagayyara.

Binciken BBC na malama jami'a masu lalata dalibai

A Najeriyar, an yi ta ce-ce-ku-ce a kan wani binciken da BBC ta yi, inda ta bankado wasu malamai da ke lalata da dalibai mata domin su yi musu alfarma a karatunsu.

Rahoton ya haddasa muhawara sosai a kasar, har ta kai ga wasu jami`o`in sun dauki matakan hukunta masu aikata irin wannan laifin.

'Auren Shugaba Buhari da Sadiya Umar'

Hakkin mallakar hoto others

Wani batu na baya-bayan nan da ba za a yi saurin mantawa da shi ba, shi ne na jita-jitar da aka yi ta yadawa cewa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai angwance da Ministar ma`aikatar jin-kai ta kasar Sadiyya Faruk, har ma masu hada-wuri suka tsayar da ranar daura auren nasu.

An yi ta yada wasu hotunan ministar, ana cewa na kamun amarya ne, yayin da wasu kuma ke cewa maganar ta yi karfi har uwargidan shugaban Najeriyar, Aisha Buhari ta yi yaji.

Amma tana dawowa daga wani bulaguron da ta kai Burtaniya ta yi watsi da maganar.

Jihar Zamfara ta soke dokar fansho

A Najeriyar dai an bijiro da abubuwa masu yawa a wannan shekarar, wadanda ga alama maganarsu za ta fantsama cikin shekara mai zuwa, ciki harda batun kudin fansho na musamman din da wasu tsoffin gwamnoni suka yi wani abu mai kama da debi-da-kanka, ta hanyar tisa `yan majalisun dokokin jihohinsu a gaba wajen kafa dokar ta ba su damar karbar daruruwan miliyoyin naira a kowane wata.

Jihar Zamfara dai ta soke dokar, wadda ta bai wa tsohon gwamna damar karbar naira miliyon goma a kowane wata, kodayake na wasu jihohin ma ya ninka hakan.