Muhimman abubuwan da suka faru a Nijar a 2019

  • Daga Tchima Illa Issoufou
  • Reporter
Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Al'amura da dama ne suka faru a Jamhuriyar Nijar a 2019 tun daga kan matsalolin tsaro da hare-haren ''ta'addanci'' da suka yi sanadiyar mutuwar sojojin kasar da ma fararen hula.

Ta haka ne kuma wasu al'amuran suka faru a fannin ilimi da kiyon lafiya da noma da kiwo da siyasa har ma da tattalin arziki da dai sauransu.

An dai wayi garin sabuwar shekarar ne ta 2019 da ce-ce-ku-ce kan jawabin Shugaba Mahamadou Issoufou wanda ya ce Jamhuriyar Nijar ta samu ci gaba gagarumi a fannin tattalin arziki da sama da kashi biyar cikin dari, abin da ya zarce na kasashen ECOWAS ko CEDEAO da ke da kashi uku cikin dari.

Sai dai masana kan tattalin arziki irin su Dakta Soly Abdoulaye suka ce abu ne mai kamar wuya ga kasashen renon Faransa.

Haka zalika a farkon shekarar ce dakarun sojin sama suka wa mayakan Boko Haram luguden wuta inda suka kashe sama da 'yan bindiga 200.

Ta hakan ne kuma wasu 87 suka mutu ta dalilin barin wutar da sojojin yakin kasa suka yi, jami'an tsaron sun kuma kama kayayaki da dama daga ciki harda motoci da kwale kwale da bindigogi iri daban daban da albarusai da dai sauransu.

A bangaren dakarun kasar ba'a samu asarar rai ba ko rauni ba. 'Yan kasar sun nuna jin dadi da wannan gagarumar nasara da dakarun kasar suka samo.

Shekarar ta 2019 ta zamo shekarar da Nijar ta fusakanci yawan hare-hare daga kungiyoyin '' 'yan ta'adda,'' hare-haren da suka yi sanadiyar salwanta rayukan dakarun kasar da dama a wurare daban-daban.

Wuraren sun hada da Baley Beri kusa da Tounga Tounga inda sojoji 30 suka kwanta dama , akwai kuma taho mu gama da aka yi a Blabrine na yankin Gegimin a jihar Diffa da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kasa sama da goma.

Akwai kuma taka nakiyoyi nan da can cikin jihar Tillabéri da kuma hare-haren kauyen Inates na farko da na biyu na daga cikin tashin hankalin da kasar ta fuskanta a shekarar. Hakan ya sa 'yan kasar zubar da hawaye.

A 2019 ce kuma wata gobarar motar daukar mai ta lakume rayukan mutane da dama a garin Yamai.

Asalin hoton, AFP

Wannan ma wani karin tashin hankali ne in ji ministan cikin gida Bazoum Mohamed a yayin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru ya kuma yi wa manema labarai bayani kan faruwar lamarin tare da kira da a kiyaye.

Kan batun tattalin arziki a shekarar 2019, Jamhuriyar Nijar ta jinginar da babban otel din nan mai suna ''Hotel Gawaye,'' shi ne otel daya tal da gwamnatin kasar ta mallaka kuma ta jinginar da shi ga wasu 'yan kasuwar kasar Indiya har na tsawon shekaru 30.

Sai da mashahurin dan kasuwar nan na Nijar wato Bukari Sani Zilly ya kalubalanci wannan matakin.

A Farkon shekarar ce kuma shugaban kasar yayi wani garan bawul ga majalisar ministoci, inda ya kori Ministan Kudi Hassoumi Masaoudou.

An kori ministan ne yayin da yake wata ziyarar aiki a jihar Maradi, sai dai gwamnatin bata fito ta bayyana dalilan korar ministan ba amma 'yan kasa sun yi ta shaci fadi suna bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta game da batun.

Asalin hoton, Getty Images

Ministan cikin gidan kasar ya ce dokar da gwamnan jihar Tillabéri ya samar kan dokar ta baci ta saba wa ainahin dokar da gwamnatin kasar ta aza da kuma tanade-tanaden da tayi dan bai wa al'umomin yankunan da ke karkashin dokar ta bacin damar tafiyar da lamuran su cikin walwala.

Dokar gwamnan jihar ta Tillabéri ta takaita lokutan zirga-zirga abin da 'yan jahar suka ce akwai takura.

A shekarar 2019 ce gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta samar da rigakafin cutar sankarau ga masu shekara daya har zuwa bakwai a duniya da yawan su ya kai miliyan shida da dubu saba'in da biyu da dari takwas a fadin kasar ta Nijar.

Rigakafin kuma na zama cikon gurbi na wadanda ba su samu aka yi musu ba a 2011.

Asalin hoton, Getty Images

A 2019 dai ce 'yan asalin Damagaram musamman matasa suka yi nazari kan matsalolin da wannan jiha ke fuskanta a fannoni daban-daban inda suka fara nemo hanyoyin magance wadannan matsaloli.

Hakan ne ma ya sa matasan kafa wani kwamiti da zai jagoranci ayyukan ci gaban jihar.

Bangarori da dama da suka hada da kiyon lafiya da illimi da noma da kiyo ne za su mayar da hankali kansu.

Matsalar tabarbarewar illimi ga matasa ne abin da ya fi daukar hankalin wannan kwamiti kamar yadda Maman Laouali Ali Djibo, wanda daya daga cikin 'yan kwamitin ya shaida wa BBC.

Shekarar 2019 ta zamo shekarar da kasar ta shirya tarurruka da dama masu muhimmanci da suka hada da taron koli na shugabannin kasashen kungiyar tarrayar Afrika AU.

Taron dai ya yi nazarin wasu batutuwa masu nasaba da tattalin arzikin wannan nahiya.

Daga ciki akwai batun nan na fara aiki da yarjejeniyar cire shingayen da ke tsakanin kasashen, kan sha'anin kasuwanci don samun kasuwanci na bai daya ga nahiyar da ake kira ZLECAF.

Najeriya na daga cikin kasashen da suka nuna shakku ko dari-dari kan wannan yarjejeniya. Mustapha Suleiman shi ne Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Najeriya kuma ya shaida wa manema labarai cewa ba wani shakku ko kwankwato, Najeriya za ta mika kai bori ya hau.

A shekarar ta 2019 ce kuma aka gudanar da wani taro a Yamai da ya hada gwamnonin yankin tafkin Chadi kan batun hadin gwiwar da suka yi tsakanin su (Nasara ko akasin haka.)

Sun yi hadin gwiwar ne da zummar karfafa hanyoyin dawo da zaman lafiya mai dorewa a wannan yanki da kuma yaki da Boko Haram.

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kazalika, taron ya maida hankali kan dabarun yankin na wanzar da zaman lafiya wanda majalisar ministoci da kwamitin tafkin Tchadi da kuma kwmitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afirka suka saka wa hannu.

Kazalika an gudanar da taron ministocin raya al'adun kasashen Afirka da Caribbean da kuma Pacifique inda kasashe 51 daga cikin 79 da kungiyar ta ACP ta kunsa da suka hada da 48 na Afirka ta Kudu da hamadar Sahara.

Kasashe 16 na Caribbean da 15 na Pacifiq ne suka halarci wannan zama domin ganin kowace kasa ta Kungiyar ACP ta yi koyi da Nijar wajen bunkasa al'adu.

A fannin siyasa, shekarar 2019 ta zamo shekarar tsaida masu takarar shugabancin kasa ga jam'iyyun siyasa inda jam'iyyar PNDS Tarraya bayan ana ta tunanin ko za ta ci ko baza ta ci ba.

Ana kuma ta shaci fadin da ake cewa Shugaba Mahamadou Issoufou ba zai yarda a tsayar da Bazoum ba a matsayin wanda zai gaje shi, sai gashi ba wata gardama jam'iyya mai mulki ta mika wa Bazoum Mohammed tutarta.

Asalin hoton, Getty Images

Ita ma a nata bangaren jam'iyyar adawa ta Moden Fa Lumana ta gudanar da tarurrukan congres biyu a rana daya a jihohi daban-daban , yayin da bangaren Noma ya gudanar da nashi taro a garin Dosso, sai kuma bangaren Tahirou Parck 20 ya yi nashi congres din a birnin Yamai sai dai dukannin su sun tsaida Hama Amadou a matsayin dan takarar jam'iyyar.

A 2019 dai ce shugaban jam'iyyar Moden FA Lumana, Hama Amadou ya dawo gida bayan da ya kwashe kusan shekaru 5 yana zaman gudun hijira.

Haman dai ya dawo gida ne don ta'aziyyar mahaifiyarshi da ta rasu kafin daga bisani yake mika kanshi ga hukumomin shari'a da suka umurce shi da ya koma gidan yarin shi na garin Filinge.