Hakimin Birnin Gwari ya kubuta daga masu garkuwa

Hakimin Birnin Gwari , Alhaji Yusuf Yahaya

Asalin hoton, OTHERS

Hakimin Birnin Gwari , Alhaji Yusuf Yahaya wanda aka yi garkuwa da shi ta hanyar dasa masa bindiga ranar 18 ga watan Disambar nan, ya kubuta da safiyar yau Juma'a.

An dai yi garkuwa da Alhaji Ibrahim Yahaya a kan hanyarsa ta zuwa wani wuri da aka kebe domin yin sasanci tsakanin al'ummar Birnin na Gwari da masu sata da kisan jama'a a yankin.

Wata sanarwa da matasan yankin na Birnin gwari suka fitar, ta ce Alhaji Ibrahim Yahya ya tsira ne daga hannun masu garkuwar a daren Alhamis a kauyen Sabon Birni da ke bayan filin jirgin sama na jihar Kaduna.

Basaraken ya kuma aikewa wani makusancinsa sakon wayar hannu da misalin karfe 5:30 na asuba da ya je ya dauke shi.

Sanarwar ta kara da cewa hakimin ya tsere ne daga inda yake a tsare a lokacin da masu garkuwa da shi ke tsaka da barci.

A kwanakin baya an yi wata tattaunawar tsagaita wuta tsakanin 'yan bindiga da jami'an karamar hukumar Birnin Gwari karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar, Alhaji Garba Gambo.

Sai dai an cimma yarjejeniyar ce ba tare da karbe makaman da ke hannun 'yan bingidar ba.

Kuma wasu bangarorin 'yan bindigar sun bayyana karara cewa ba za su kasance cikin yarjejeniyar ba.

Bayanai daga mazauna yankin na nuna cewa 'yan bindigar na shawagi firi-falo da makamansu a cikin kauyuka suna gudanar da harkokinsu ba tare da shakku ko fargaba ba.