Lafiya Zinariya 'Abin da ke janyo bari ga masu ciki

Bayanan sauti

Lafiya Zinariya 'Abinda ke janyo bari ga masu ciki

Latsa wannan alamar lasifikar domin sauraron Dr Mairo Mandara kwararriyar likitar mata.

Dr Mairo ta ce abin da ake nufi da bari shi ne idan an samu ciki sai ya zube kafin dan tayi ya kai munzalin yin rai, kuma wannan lokaci a likitance wata shida ne.

Bari ya na zuwa daban-daban, tun da fari sinadarin kwakwalwa shi ke rike da ciki idan aka samu sauye-sauye na sinadarin ya zamanto ba dai-dai yake ba to yana janyo bari.

"Yawanci barin ciki dan watanni uku da mata ke yi rahama ne, saboda ta yiwu za a haifi dan da wata tawaya to Allah cikin ikonsa sai ya barar da shi tun ya na karami."

Wadansu matan bakin mahaifarsu a bude yake, idan jariri yana girma yana kara kusanto bakin mahaifar idan ba a yi gaggawar zuwa asibiti an dinke ba, mace za ta iya bari.