Faduwar wasu ce ta zo ba Kannywood ba - Naziru

Latsa wannan alamar lasifikar da ke sama domin sauraren Naziru Sarkin Waka.

Fitaccen mawakin nan na masana'antar Kannywood, Naziru M Ahmad, ya musanta rade-radin cewa masana'antar fina-finan Hausar na shirin durkushewa.

Sarkin Wakar Sarkin Kano ya ce karshen wasu ne ya zo, don haka suke ganin masana'antar ce ta ke gab da rugujewa.

Ya kara da cewa zamani ne ya cimma wasu, idan aka yi duba da yadda masana'antar take a baya da yanzu yawancin masu shirya fina-finai na zamanin nan a baya ba bakin komai suke ba.

Naziru ya ce dama can an kafa Kannywood babu shugabanci, kamar gida ne aka share fili aka dora. Don haka wasu ma nan gaba za su kawo irin nasu tsarin a haka za a yi ta tafiya.