Kada mu yarda 'yan ina-da-kisa su raba kanmu - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

''Yan IS gungun 'yan ina-da-kisa ne kawai da ke bata wa addinin Musulunci suna'

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da kisan da 'yan kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci a Afirka ta yamma suka yi wa wasu kiristoci 11, wanda aka nun a wani bidiyo da kungiyar ta wallafa.

Buhari ya kuma yi kira ga 'yan kasar da kada su bari 'yan ta'adda su raba kawunansu, sakamakon yadda maharan suke farwa mabiya wasu addinan.

A bidiyon da IS ta fitar a lokacin bukukuwan Kirsimeti, kungiyar ta ce ta kashe kiristocin ne don daukar fansa kan kisan da aka yi wa shugabanta Abubakar Albaghdadi a watan Oktoba, yayin wani hari da Amurka ta kai maboyarsa.

"Na kadu kuma na damu matuka da kisan Kiristocin, mutanen da ba su ji ba su gani ba a hannun marasa imani, da ba sa tsoron Allah, gungun 'yan ina-da-kisa da ke bata wa addinin Musulunci suna," in ji Buhari.

A wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya kara da cewa "ka da mu taba bari 'yan ta'adda su raba kanmu ta hanyar hada Musulmi da Kirista fada da juna, saboda wadannan makasan ba musulunci suke wakilta ba, ba kuma miliyoyin musulmai masu bin doka da oda a fadin duniya suke wakilta ba."

Shugaban na Najeriya ya kara da cewa, babu wani musulmin kirki da zai dinga cewa "Allahu Akbar" yayin da yake kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. A cewar shugaban Kur'ani ma ya yi Allah-wadai da hakan.

Ya kuma jaddada kudurinsa na yakar 'yan ta'adda, tare da karfafa hadin kai da sauran kasashe wajen karya kashin bayan 'yan ta'addar.

A 'yan kwanakin nan dai kungiyoyi masu da'awar jihadi sun kara matsa kaimi wajen kai hare-hare a yankin Afirka ta yamma.

A cikin wata guda, mayakan sun kashe sojoji da 'yan sanda da farar hula fiye da 100 a Niger da Mali da Burkina Faso da Najeriya.

Hukumomin Najeriya sun sha ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram, sai dai har yanzu suna kai munanan hare-hare kan cibioyin sojoji da fararen hula.

A tsakiyar watan Dismba, kungiyar ta fitar da wani bidiyo na kisan wasu ma'aikatan kungiyar agaji ta Action Against Hunger su hudu, abinda ya janyo mummunan martani.

Haka kuma a watan Dismbar mayakan sun yi wa sojoji kwanton bauna a Damboa ta jihar Bornon Najeriya, inda suka kashe sojoji 10.

Ko a baya-bayannan sai da gwamnan jihar Borno ya yi kira ga sojojin kasar da su kwato wasu garuruwa dake hannun Boko Haram a jihar ta Borno.