Wolves ta kafa tarihi a kan Guardiola da cin Man City gida da waje

Wolves ta farafdo daga 2-0 inda da doke Manchester City 3-2 a filin wasanta na Molineux.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wolves ta farafdo daga 2-0 inda da doke Manchester City 3-2 a filin wasanta na Molineux.

Wolves ta farfado daga 2-0 inda da doke Manchester City a filin wasanta na Molineux, a wasan da kuma ta kafa tarihin yi wa kociyan City, Pep Guardiola ci gida da waje.

Tun a minti na 12 ne mai tsaron ragar City Ederson ya karbi jan kati, bayan keta a kan Diogo Jota.

To amma duk da haka wasan bai fito da wallen kungiyar ba, don kuwa a hakan ta saka wa Wolves kwallaye biyu ta hannun Raheem Sterling.

To amma bayan da Wolves din mai masaukin baki ta yi kukan kura ne ta farke wasan ta hannun Adama Traore da Raul Jimenez kafin Matt Doherty ya tabbatar da samun nasara gida da waje a kan Manchester City da Guadiola.

A yanzu Wolves ta kafa tarihi a matsayin kungiya ta farko a Ingila da ta taba doke Guardiola gida da waje.

Idan za a iya tunawa Wolves ta lallasa City 2-0 a wasannin farko na gasar.

Rashin nasarar City na nufin Liverpool ta kara nisa a gasar firimiya da maki goma sha uku, yayin da Wolves ta fara jin kanshin zuwa gasar Zakarun Turai.

A yanzu City tana ta uku a kan teburi da maki 14 tsakaninta da Liverpool da ke da kwantan wasa daya.

Bayanan hoto,

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da na'urar VAR ke haifar da matsala a wasanni.

Wasan ya fuskanci cikas bayan da na'urar da ke tantance abin da ya faru wato VAR ta soke bugun fanaretin da mai tsaron ragar Wolves ya riga ya ture, inda ta umurci Sterling da ya sake bugawa, wai saboda 'yan wasan bayan Wolves da ke dako sun yunkuro a lokacin da zai buga.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da na'urar VAR ke haifar da matsala a wasanni.

Dama dai tuni an fara kira da a kara sarrafa na'urar ganin irin yadda take ta kura-kurai da sukan haddasa ce-ce-ku-ce.

Wasanni da za'a yi yau Asabar

Brighton da Bournemouth

Newcastle da Everton

Southampton da Crystal Palace

Watford da Aston Villa

Norwich da Tottenham

West Ham da Leicester

Burnley da Man Utd