Shugaban kasa ya rage albashinsa domin talakawa

Mr Lungu ya ce matakin sadaukarwa ne ga talakawa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mr Lungu ya ce matakin sadaukarwa ne ga talakawa

Shugaban Zambia Edgar Lungu ya zaftare albashin manyan ma'aikatan gwamnati yayin da kasar ke fuskantar tsadar man fetur da wutar lantarki.

Mr Lungu ya ce matakin sadaukar da wani bangare na albashinsa da kuma na sauran manyan jami'ai da ya kai kashi 10 zuwa 20 cikin dari zai fara aiki ne nan take.

Shugaban ya ce ya yi la'akari da irin matsin rayuwa da 'yan kasar ke ciki kuma kudin da za a tara zai tafi ne kacokan ga tallafa wa marasa karfi a cikin al'umma.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Lauyan mai shekara 72 ya zama shugaban kasa ne a watan Janairu na 2015 a zaben da aka kira bayan mutuwar Shugaba Michael Sata

A ranar Alhamis din da ta gabata ne man fetur da kuma kudin wutar lantarki su ka tashi da kashi 10 cikin 100.

An kuma yi hasashen cewa kudin wutar zai ninka a farkon shekara mai kamawa.

Ana ci gaba da samun ra'ayoyi daban-daban a kafafen sada zumunta musamman daga 'yan kasar dangane da wannan mataki na shugaban kasar ta Zambia ya dauka