An yi gagarumin kamu na hodar koken da za a kai makwabciyar Najeriya

Tarin hodar Iblis ta koken da aka kama a Uruguay za a kai Togo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kama hodar Iblis ta koken din ne wadda za a kai Togo, a cikin garin fulawar waken suya

Hukumomi a Uruguay sun ce sun yi wani wawan kamu da ba su taba yin irinsa ba a tarihin kasar, na hodar Iblis ta koken (cocaine) wadda nawinta ya kai kusan tan hudu da rabi.

A baya bayan nan ana ci gaba da amfani da kasar ta Uruguay a matsayin wata hanya ta wucewa da hodar Iblis ta koken da ake samarwa a kasashen Latin Amurka, ake kai wa kasashen Turai da Afirka.

Wannan tarin hodar dai an boye shi ne a sundukai ko kwantainoni da ke dauke da buhunan garin fulawa da za a kai Lome, babban birnin kasar Togo.

An kiyasta kudin hodar a banza-banza ya kai kusan dala biliyan daya.

An kama ta ne a wani aikin bincike na hadin guiwa tsakanin sojin ruwa da hukumar kwastan ta tashar jiragen ruwa ta babban birnin kasar ta Uruguay, Montevideo.

A watan da ya gabata ma a wannnan tashar jiragen ruwan ta babban birnin kasar ta Uruguay, an gano wata kwantaina dauke da koken da nauyinta ya kai tan uku, wadda za a kai Jamhuriyar Benin mai makwabtaka da Najeriya.

Wadannan manyan kamen biyu da aka yi na hodar koken (Cocaine), sun biyo bayan kama wata kwantaina da aka yi ne a watan Agusta a Jamus, wadda ke dauke da tan hudu da rabi na hodar, wadda aka kai Hamburg daga Uruguay.

Gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokinta na tudu da makwabtanta, sakamakon satar shiga da miyagun abubuwa ciki har da makamai da kuma sumogal na kayan abinci musamman shinkafa da ake yi zuwa cikin kasar.

Wannan mataki da Najeriyar ta dauka ya jawo durkushewar harkokin kasuwanci na wasu makwabtanta, da ke cin ribar shigar da kayayyakin da ake yi daga cikinsu zuwa Najeriyar.

Hukumomin kasar mai karfin tattalin arziki a Afirka sun ce rufe kan iyakokin da suka yi na watanni yana matukar amfani da tasiri ta fannin bunkasa harkokin mutanenta na gida da dakile fasa-kwauri da shiga da miyagun abubuwa cikin kasar.