Mutum 76 sun mutu a harin bam a Somalia

Ana kokarin garzayawa da wani mutum zuwa asibiti bayan harin Mogadishu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutane da dama sun samu munanan raunuka a harin

Akalla mutum 76 ne aka kashe a wani harin mota da aka makare da bam a Mogadishu babban birnin Somalia.

Motar ta yi bindiga ne a wani shingen binciken ababen hawa da ke kusa da wata mahada a lokacin cinkoson ababen hawa.

Daraktan asibitin Madina da ke Mogadishu Dakta Mohammed Yusuf ya tabbatar da karbar gawa 73 a asibitin.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma kungiyar al-Shabab na yawan kai hare-hare a yankin.

Kungiyar al-Shabab mai biyayya ga kungiyar al-Qaida ta yi fiye da shekara 10 tana tayar da kayar baya a Somalia.

A shekarar 2011 ne dakarun gwamnati suka fatattaki mayakan al-Shabab daga Mogadishu. Sai dai kungiyar na ci gaba da nuna iko a wasu yankunan kasar.

Abin da shaidu suka gani

"Sai gawarwarki nake ta gani ta ko'ina...a lokacin da abin ya fashe. Wasu daga cikinsu sun kone kurmus," inji Sakariye Abdukadir, wanda ke kusa da wurin da bam din ya fashe.

Wani dan majalisar dokokin Somalia Mohamed Abdirizak ya ce wandanda suka mutu sun kai mutum 90. Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da adadin ba.

"Allah Ya jikan wadanda wannan hari na dabbanci ya yi ajalin su da rahama," a cewar tsohon ministan tsaron cikin gidan kasar.

Map

Rahotanni na cewa daliban jami'a ne yawancin wadanda suka mutu a harin.

Wasu daga cikin shaidun gani-da-ido sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa motar ta fashe ne a kusa da wasu injiniyoyi 'yan kasar Turkiyya da ke aikin gyaran titi.

Ministan harkokin wajen Somalia Ahmed Awad ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa biyu daga cikin injiniyoyin 'yan Turkiyya sun rasu a harin.

Yawancin mamatan daliban jami'a ne "masu burin zama wani abu nan gaba da kuma maza da mata hazikai", kamar yadda ya rubuta a shafin nasa.

Turkiyya na daga cikin manyan masu taimaka wa Somalia tun bayan farin da aka samu a kasar a 2011.

A farkon watan nan na Disamba kuniygar al-Shabab ta kashe mutum biyar a harin da kungiyar ta kai wa wani babban otal da 'yan siyasa da jakadun kasashe da kuma manyan hafsoshin soji ke zama.