Halin da firamaren farko a Kano ke ciki bayan shekara 100

Makarantar firamare ta Shahuci a Kano
Image caption A shekarar 1919 aka kafa makarantar firamaren ta Shahuci

A yau ne makarantar firamare ta farko a jihar Kanon Najeriya ke cika shekara 100 da kafuwa.

A shekarar 1919 ne aka bude makarantar firamare ta Shahuci da ke kwaryar birnin Kano a arewacin Najeriya.

Ita ce makarantar firamare ta farko da aka kafa kuma ta samar da 'yan boko masu yawa a jihar Kano.

An kafa ta ne da nufin samar da wadanda za su zama malamai a makarantun da za a bude daga baya a sassan jihar.

Yanzu makarantar mai shekara 100 na bukatar gyare-gyare da za su ci akalla naira miliyan 53, a cewar shugaban tsoffin daliban makarantar, Abubakar Ibrahim Yakasai a hirarsu da Khalifa Shehu Dokaji.

"Makarantar ta tsinci kanta a halin ne sakamakon gibi da aka samu tun daga lokacin da ta cika shekara 70, inda daga nan ne tsoffin daliban suka yi sanya wurin tallafa mata," in ji Abubakar Ibrahim.

Ya ci gaba da cewa: "Yanzu tsoffin daliban makarantar na shirin daukar nauyin kula da makarantar da kuma samar da kayan karatu ga dalibai.

"Wannan makarantar ta Shahuci ta taka muhimmiyar rawa wurin bunkasa harkar ilimin boko da kuma yada shi a jihar Kano.

"Yanzu makarantar mai shekara 100 na bukatar gyare-gyare da za su ci akalla naira miliyan 53."

Ya ce yawancin daliban makaratar su ne suka fara zama malamai da shugabanni a sauran makarantun firamare da na sakandare da aka bude a larduna da gundomomi da kauyukan jihar a wancan lokaci.

Daga cikin fitattun daliban Firamaren Shahuci akwai Dan Masanin Kano, Dr Yusuf Maitama Sule, Engr. Balarabe Isma'il da marigayi Ambasada Shu'aibu Usman Yola tsohon mataimakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya.

Sauran sun hada da shugaban firamare ta Dala na farko Dankadai Muhamamdu, wanda ke daga cikin daliban da aka fara yayewa bayan an bude makarantar da su a shekarar 1919.

An bude makarantar Shahuci ne bayan bude makarantar gidan Dan Hausa, wadda aka kafa ta a kwaryar birnin Kano domin samar da mutanen da za su yi aiki a matsayin marabuta da akawun kotunan alkalai da fadar sarakuna.

Labarai masu alaka