Gane Mani Hanya: Yadda ya kamata a haka rijiyar burtsatse

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar Ahmad Abba da Alhaji Abubakar Musa Maa-chii-ka

A makonnin baya ne kungiyoyin masu haka rijiyoyin burtsatse daga kasashen duniya daban-daban suka yi wani taro a birnin London, domin kyautata alaka tsakaninsu.

Alhaji Abubakar Musa Maa-chii-ka, mataimakin shugaban kungiyar AWDROP (audurop) reshen arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin mahalarta taron.

Cikin tattaunawarsa da Ahmad Abba Abdullahi, Alhaji Abubakar ya bayyana yadda ya kamata a rika haka rijiyar burtsatse.

Kazalika, ya yi bayani game da bambancin da ke tsakanin rijiyar burtsate da ta gargajiya.