Kauyukan Zamfara sun koka kan hare-haren 'yan bindiga

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle Hakkin mallakar hoto @Bellomatawalle1

Wasu al'umomin kauyuka a yankunan jihar Zamfara sun koka kan yadda mahara ke ci gaba da kai musu hari, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar ke ikirarin cewa ta cimma da maharan a watannin baya.

Mutanen kauyukan Dankurmi, da Zargado da Danhayin Zargado Farar Kasa da ke karkashin masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru sun ce maharan na cin karensu ba babba dauke da makamai, abin da ke razana jama'a.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa "cikin kwana biyu maharan sun kwashe shanu fiye da 600 a Dankurmi, kuma an kashe mutum biyu da wani likita da ke kula da lafiyar alummar garin."

Ya kuma ce a Dan ma'aji 'yan bindigar sun kashe wani shugaban 'yan sa-kai, haka ma a garin Farar Kasa sun harbi wani sanannen dan sa-kai da ake kira mai bataliya, "yanzu haka yana can kwance a asibiti yana karbar magani," in ji shi.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya ce suna daukar matakai domin kawo karshen matsalolin kuma a cewarsa "wannan ba matsala ba ce da za a magance ta a dare daya."

"Kwata kwata sasancin nan bai yi wata shida ba, yana da wahala a iya magance barnar da aka shafe wata goma ana yi a wata shida, in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

An shafe shekaru Jihar Zamfara na fama da har-haren 'yan bindiga masu fashin shanu da satar mutane.

A kwanakin baya ne Kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin gano tushen matsalar tsaron jihar ya ce gwamnatin ta gaza wajen aiwatar da shawarwarin da ya bayar.

Kwamitin na mutum tara karkashin jagorancin tsohon sufeto janar na 'yan sandan Najeriya MD Abubakar, ya ce sama da wata biyu kenan da gabatar da rahoton ga gwamnan Jihar Bello Matawalle amma ba abin da aka yi.

Daga cikin manyan shawarwarin da kwamitin ya bayar sun hada da tube wasu manyan sarakunan gargajiya guda biyar da uwayen kasa 33 da kuma Hakimai da dama wadanda kwamitin ya zarga da hannu a kashe-kashen jihar da satar mutane domin kudin fansa.

Akwai kuma jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kwamitin ya zarga tare da bayar da shawarar a hukunta su.

Dakta Sani Abdulahi Shinkafi daya daga cikin mambobin kwamitin, ya shaida wa BBC cewa jan kafar ya nuna cewa gwamnatin jihar ta Zamfara ba da gaske take ba.

"An kafa kwamiti an kashe kudin mutane kuma an kasa aiwatar da rahoton da aka bayar," in ji shi.

Sai dai kuma gwamnatin Zamfara ta ce tana nazari ne kan rahoton, kuma idan ta kammala za ta aiwatar da dukkanin shawarwarin da kwamitin ya batar.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Zailani Baffa ya shaida wa BBC cewa ba za a yi gaggawar aiwatar da rahoton ba tare da nazari ba.

A cewar Zailani, gwamnatin Matawalle tana nazarin rahoton kuma za ta aiwatar ba tare shiga hakkin kowa ba, sai dai bai fadi lokacin da za ta kammala nazarin rahoton ba.

Labarai masu alaka