'An fi kisan jama'a a shekarar 2019 a Amurka'

Akalla mutum 22 aka kashe a harin El Paso a Texas a watan Agusta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akalla mutum 22 aka kashe a harin El Paso a Texas a watan Agusta

Wasu alkalumman bincike daga bayanan da aka tattara a Amurka sun nuna cewa shekarar 2019 ce mafi muni da aka fi kisan mutane ta hanyar bude wa taron jama'a wuta fiye da ko wane lokaci tun fara tattara bayanan shekaru da suka gabata.

Binciken wanda kamfanin dillacin labaru na AP da USA Today da kuma jami'ar Northeastern suka gudanar ya tattara bayanai ne daga abubuwan 41 da suka faru, da suka shafi mutuwar sama da mutum 200.

Kashe-kashen a binciken na nufin duk inda aka kashe mutum hudu ko fiye a lokaci guda.

Binciken ya bi diddigin kashe-kashen da suka faru ne a Amurka tun 2006, kuma sakamakon binciken ya ce shekarar 2019 ne aka fi yawan kashe jama'a lokaci guda inda yawan wadanda aka kashe a shekarar suka kai 224 fiye da adadin wadanda aka kashe a 2017 inda aka kashe mutum 211.

Shekarar 2017 ce binciken ya ce aka bude wa taron jama'a wuta mafi muni a tarihin Amurka, inda aka harbe mutum 59 a wani taron biki a Las Vegas.

Daga cikin mafi muni a 2019 shi ne kisan mutum 12 a Virginia a bakin teku a watan mayu da kuma mutum 22 da aka harbe a El Paso a Agusta. Kuma jihar California ce binciken ya ce aka fi kashe mutane fiye da sauran jihohin Amurka.

Binciken ya ce akwai kashe-kashen mutane a Amurka da ba su shiga kanun labarai ba saboda sun shafi ringingimu 'yan uwa da masu hada-hadar muggan kwayoyi, da ba su bazu ba suka shafi al'umma ba.

Yawan budewa taron jama'a wuta ya karu a Amurka a cewar masu binciken duk da an samu raguwar yawan kisan mutum daya da ake samu.

Duk da wannan, amma yunkurin takaita mallakar bindiga ya cutura.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kisan jama'a na jefa mutane cikin jimami

Hakkin mallakar bindiga na kunshe a kundin tsarin mulkin Amurka da aka yi wa gyaran fuska, amman karuwar kisan jama'a bai zama dalilin da zai sa 'yan majalisar dokokin Amurka yin garanbawul ga batun mallakar bindiga ba a kasar.

A watan Agusta da aka kai munanan hare hare a Ohio da El Paso da Texas, shugaba Trump ya ce za a yi muhimmayar tattaunawa tsakanin shugabannin majalisa kan mallakar bindiga.

Akwai wasu daga cikin Jiga-jigan jam'iyyar Democrats mai hamayya da suka bukaci daukar mataki kan mallakar bindiga, kuma dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden na daga cikinsu, wanda ke son haramta kerawa da sayar da bindigogi tare da sa ido ga sayar da bindigogin.

Haka ma Elizabeth Warren ta yi alkawalin rage yawan kashe-kashe ta hanyar bindiga da kashi 80.

Labarai masu alaka