An kai wa Yahudawa hari a Amurka

'Yan sanda sun killace wurin da abin ya faru a kusa da cocin synagogue

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun killace wurin da abin ya faru a kusa da cocin synagogue

Wani mutum dauke da adda ya kafta wa akalla mutum biyar wuka a wurin wanin bikin mabiya addinin yahudu.

Maharin ya sari daya daga cikin mutanen da lamarin ya ritsa shi akalla sau shida kafin ya tsere.

Ya kai harin ne a inda iyalan gidan wani malamin addinin yahudu suka shirya wani bikin addininsu da ake kira Hanukkah a birnin New York na kasar Amurka.

Mutumin ya tsare kafin daga bisani 'yan sanda su yi nasarar cafke shi. Har yanzu ba'a riga an gano dalilinsa na kai harin ba.

Harin na zuwa ne kwana daya bayan 'yan sanda a birnin na New York sun ce suna tsananta sintiri a yankunan da ke da yawan mazauna Yahudawa sakamakon karuwar barazana da hare-haren kin jinin yahudawa a kasar.

Abin da ya faru

Aron Kohn dan shekara 65 wanda ya je halartar bikin, ya ce da shigar mutumin kofar gidan sai ya fara saran mutane da adda, ba wanda ya iya tinkararsa. Kowa ta kansa yake yi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Akwai yahudawa masu ra'ayin rikau da dama a yankin Monsey

Kohn ya ce mutumin ya yi kokarin shiga cikin wani wurin ibadar da ke gidan amma mutanen da ke ciki suka kulle kofar.

Mutumin ya tsere a cikin wata mota amma wadanda abin ya faru a kan idonsu sun dauki lambar motar.

Daga baya 'yan sanda sun ce sun gano motar kuma sun kama wani da ake zargi.

Wane martani ake mayarwa?

Gwamnan New York Andrew Cuomo ya yi tir da harin wanda ya ce harin ragonci ne.

"Mun yi tir da duk wani nau'in kyamar Yahudawa da nuna wariya wadanda suka saba wa tsarin rayuwarmu ta zaman tare. Muna Allah-wadai da wannan aiki na nuna tsana", kamar yadda wata takarda da ya fitar ta ce.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan sanda a New York sun fara tsaron synagogue saboda karuwar muggan laifuka

Yahudawa na yin bikin Hanukkah domin murnar nasarar da Judah Maccabee ya samu a kan Girkawan a Syria a karni na biyu kafin zuwan Annabi Isah da kuma sake kwato birnin Urushalima.