Shigar banza: An hukunta mutum 200 a Saudiyya

'Yan sandan Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan sandan Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun kama mutum 200 da zargin karya dokokin mu'amala da kamun kai a bainar jama'a.

'Yan sandan kasar sun ce laifukan da mutanen suka aikata sun hada da shigar banza da cin zarafi mata.

Wannan shi ne karon farko da jami'an kasar suka yi irin kamun tun bayan da gwamnatin kasar ta fara sassauta yanayin gudanar da harkoki a kasar.

'Yan sandan kasar sun ce an yi wa mutanen horo daban-daban gwargwadon laifukan da suka aikata.

Hukumomin kasar sun kuma tsare wasu mutum 88 saboda aikata laifn cin zarafin mata.

An tsare mutanen ne bayan wasu mata sun yi korafin cewa sun ci zarafin su a lokacin wani casu da ka yi a birnin Riyadh.

Shagalin wanda dubban mutane suka halarta shi ne mafi girma a da aka taba yi a kasar.

Karon farko ke nan da aka yi irin wanna kame bayan yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ya fara sassauta dokokin kasar da suka haramta wa mata tuki da haramta gidajen sinima da harkokin wasanni da cudanyar maza da mata.

Kashi daya bisa ukun 'yan kasar wadanda yawancinsu matasa ne 'yan kasa da shekara 30 sun yi maraba da sauyin da yariman ya kawo.

Amma a watan Satumba kasar ta sanar da cewa za ta hukunta masu karya dokokinta na kamun kai a bainar jama'a.

Dokokin sun haramta yin shigar banza da kuma yin kwarkwasa ko mu'amalar tsakanin jinsi a bainar jama'a.

Dokar ta kuma haramta wa mata da maza sanya matsattsun kaya ko tufafi masu dauke da munanan hotuna ko kalamai. Wajibi ne kuma mata su rufe kafadunsu da gwiwowinsu.

An sanar da sabuwar dokar ne jim kadan bayan kasar ta fara bayar da takardar biza ga masu yawon bude ido a karon farko.

A watan Afrilu sabuwar ta haifar da rudani. Wasu ke ganin dokar ta yi harshen damo wurin fayyace haddinta. Wasu kuma na ganin za ta iya dawo da sanya ido a kan harkokin mutane wanda dokar ke neman sassautawa.

A baya an yi ta tsoron jami'an hisbah a kasar. 'Yan Hisbah su rika tisa keyar mutane daga kantuna su je masallaci kuma suna yin kashedi ga masu mu'amala da tawa ajinsi a fili.

Sai dai yanzu ba'a fiye ganin jami'an na Hisba a kasar ba bayan kafa sabbin dokokin.