Saudiyya ta yanke wa wanda ya kai wa mawaka hari hukuncin kisa

@

Asalin hoton, FAYEZ NURELDINE

Wata kotu a Saudiyya ta yanke wa wani dan kasar Yemen hukuncin kisa.

Kotun ta yanke wa mutumin hukunci ne bayan samunsa da lafin kai wa wata tawagar 'yan rawa 'yan kasar Sifaniya hari da wuka a birnin Riyadh.

Mutumin ya daba wa akalla mutum hudu daga cikin 'yan tawagar wuka, kamar yadda hukumomin kasar Sifaniya suka bayyana.

Kotun ta kuma yanke wa abokin maharin daurin shekara 12 da rabi a kurkuku.

Ana zargin mutanen da aka yanke wa hukuncin da kai hari na ranar 11 ga watan Nuwamban 2019 da alaka da kungiyar al-Qa'ida.