Bayan shekara 57 Karkandan da ya fi dadewa a duniya ya mutu

Masu kula da gandun daji a Ngorongoro sun ce Fausta ne karkanda da ya fi dadewa a duniya
Image caption Masu kula da gandun daji a Ngorongoro sun ce Fausta ne karkanda da ya fi dadewa a duniya

Karkandan da ya fi dadewa a duniya ya mutu bayan shekara 57 a duniya.

Dabbar wadda aka rada wa suna Fausta ta bar duniya tana da shekara 57 da haihuwa a Tanzania.

An fara ganin Fausta wadda bakar karkanda ce a shekarar 1965 a dajin Ngorongoro a lokacin tana 'yar shekara uku.

Ta shafe shekara 55 tana gudanar da rayuwarta ba tare da wata takura ba dajin.

Bayan tsufanta ta yi fama da rashin lafiya abin da ya sa aka dauke ta zuwa wurin killace dabbobi domin ba ta kulawa ta musamman.

Fausta ba ta da kaho, abin da wasu masana gandun daji a Ngorongoro ke ganin ya taimaka wajen tsawon kwananta.

A shekarar 2016 ne Fausta ta fara samun matsalar gani baya ga illla da ta samu sakamakon farmakin da kuraye suka sha kai mata.

"Miyagun dabbobi musamman kuraye sun fara kai mata hari kuma ta samu munanan raunuka," inji Dokta Freddy Manongi, "Zuwa shekarar 2016 dole muka dauke ta daga daji muka mayar da ita inda aka killace ta domin ba ta kulawa ta musamman.

Ya ce Fausta ce karkanda da ta fi dadewa a duniya, kuma ta mutu ne ba tare da wata matsala ba. Likitan ya ce an haifi wani karkanda a ranar da Fausta ta rasu.

Manongi ya ce karkanda ba su fiye 43 ba cikin jeji ko shekara 50 idan an killace su.