A faro titin jirgin kasa na Legas daga Kano – Dattawan Arewa

Ma'aikatan titin layin dogo a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnatin Najeriya ta ce tuni aikin layin dogon ya kawo Ibadan daga Legas

Kungiyar Tuntuba ta Arewa a Najeriya ACF ta koka game da yadda ake aikin titin jirgin kasa wanda zai hade jihar Kano da Legas, inda ta ce ya kamata a samu daidaito.

Kamnfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito AFC na cewa maimakon fara aikin da aka yi ta bangaren Legos kadai a halin yanzu, kamata ya yi a dauko aikin daga bangaren Kano ma ta yadda za a hade titin jirgin ta tsakiya.

A wata takardar da sakataren yada labaran kungiyar Muhammad Ibrahim ya fitar, ACF ta nuna muhimmancin gwamnatin kasar ta mayar da hankali wurin kawar da matsalolin tsaro.

Tuni gwamnatin Najeriya ta ce aikin layin dogon da aka faro daga Legas ya kawo Ibadan, inda aka gama shimfida kwangiri.

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ce yanzu abin da za su mayar da hankali a kai shi ne gina kananan tashoshin jirgi da ke kan hanyar.

Dattawan sun kuma bukaci gwamnatocin kasar su koma amfani da fasahar zamani wurin yakar matsalar tsaro a yankin.

Kazalika, sun jaddada muhimmancin gwamnatoci su ba da cikakkiyar kulawa ga jin dadin jami'an tsaro da ba su kwarin gwiwar gudanar da aikinsu.

Sun bayyana cewa shugabannin su aiwatar da kasafin kudin 2020 yadda ya kamata domin inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Suna masu cewa bayan rattaba hannun a kan kasafin kudin, abin da 'yan kasa ke jira shi ne gwamnati ta aiwatar da dukkan ayyukan da aka yi wa kasafin yadda ya kamata domin saukaka masu halin da suke ciki.

Kungiyar ta kara da cewa abin da 'yan kasar suka fi bukata shi ne ababen more rayuwa dangin wutar lantarki da hanyoyi da inganta harkar noma da samar wa matasa ayyukan yi da bunkasa bangaren ma'adanai.